Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
Published: April 3, 2026 at 10:02 AM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: April 3, 2026

Gwamman kwararru a fannin dokokin kasa da kasa a Amurka sun sa hannun kan budaddiyar wasika dake cewa harin da Amurka ta kaiwa Iran zai iya zama laifi na karya dokar yaki, bayan da shugaba Donald Trump ya jaddada barazanar sa a wannan makon na kai hari kan cibiyar makamashi, da cibiyar tace ruwan sha ta Iran.

Fiye da kwararru 100 a fannin dokokin kasa da kasa a Amurka, ciki har da wadanda suka fito daga manyan jami’o’i kamar su Havard, Yale, Stanford, da jami’ar Califronia, sun bayyana a wasikar da aka wallafa a ranar Alhamis cewa a abinda dakarun Amurka ke aikatawa, da furucin da manyan jami’an ta ke yi, akwai damuwa kwarai na cewa An karya dokar kasa da kasa na kare hakkin dan adam, da kuma dokokin agaji, ciki har da karya dokokin yaki.

Wasikar musamman ta lura da furucin da Trump yayi a tsakiyar watan Maris, inda yace Amurka zata kaiwa Iran hari don jin dadi kawai. Ta kuma ambaci furuci daga sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth a farkon watan Maris inda yace America bata bin sakarkarun dokokin yaki.

Kwarrarun sun nuna damuwar su kwarai kan hare-hare da aka kai kan makarantu, wuraren kiwon lafiya da gidaje.

Amurka, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
Next Post: Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar

Karin Labarai Masu Alaka

Gwannatin Jihar Kebbi Ta Arawa Maniyyata Kuɗin Aikin Hajji 2026, Labarai
An Kubutar Da Wani Wanda Mahaifinsa Ya daure Da Sarka Tsawon Shekaru 17 A Bauchi Labarai
Rashin Kyawun Hanyoyi Babbar Matsalace A Najeriya Afrika
Kayan Jinya Da Ayyukan Kiwon Lafiya Suna Barazanar Karewa A Sudan Kiwon Lafiya
Adamu: “Yakar Cin Hanci Daga Tushe Itace Mafita Daya Tilo” Labarai
Hukumar Tsaron Teku A Libya Tafara Janye Jirgi Mai Dauke Da Iskar Gas Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Sojojin Najeriya Sun Kashe Fitaccen ’Yan Bindiga Kallamu A Jihar Sakkwato Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Tattalin Arzikin Najeriya Ya Farfardo Bisa Samun Wasu Sauye Sauye Labarai
  • Kasar Togo Ta Kori Paul Henri Damiba Zuwa Kasar Sa Ta Haihuwa Afrika
  • Amurka Tasakawa Sojin Rwanda Takunkumi Afrika
  • Shugaba Trump Yace Zai Dakatar Da Kai Hari Cibiyar Makamashin Iran Afrika
  • Gwamnatin Gombe Ta Kulla Yarjejeniyar Da New Zealand Kimiya
  • Jirage Marasa Matuka Sun Kaiwa Jiragen Ruwan Mai Hari A Gulf Afrika
  • Kasar Gambiya Ta Gayawa Kotun MDD Shirin Myanmar Akan Musulmai Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.