Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Ma’aikatar Tsaron Amurka Zata Kara Samar Da Makamai
Published: March 26, 2026 at 6:29 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ma’aikatar Tsaron Amurka, wato Pentagon, ta bayyana a ranar Laraba cewa ta cimma yarjejeniyoyin tsari da kamfanonin BAE Systems, Lockheed Martin da kuma Honeywell domin ƙara yawan samar da makamai da harsasai, a wani yunkuri na mayar da rundunar sojin Amurka cikin yanayin “shirin yaki.”

Sanarwar na zuwa ne sama da makonni uku bayan Shugaban Amurka Donald Trump tare da Isra’ila sun kaddamar da yaki da Iran.

Haka kuma, ya biyo bayan ganawar da Trump ya yi a farkon wannan watan da shugabannin kamfanonin tsaro guda bakwai, yayin da Pentagon ke kokarin cike gibin makaman da suka ragu sakamakon hare-haren Amurka a Iran da sauran ayyukan soji na baya-bayan nan.

Pentagon din na kuma shirin tura dubban sojojin sama zuwa yankin Tekun Fasha domin bai wa Trump karin zabin bada umarnin kai harin kasa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito a ranar Talata.

A karkashin yarjejeniyoyin, bangaren sararin samaniya na kamfanin Honeywell zai ƙara hanzarta samar da muhimman kayayyakin haɗa makamai na ajiyar Amurka, a wani bangare na zuba jarin dala miliyan 500 na tsawon shekaru da dama, kamar yadda Pentagon ta bayyana.

Amurka, Labarai, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Netanyahu Yayi Gaggawar Amincewa Da Kasafin Kudin Kasar
Next Post: Kasar Mauritius Zata Rage Amfani Da Makamashi

Karin Labarai Masu Alaka

Hawan Nasarawa A Jihar Kano Afrika
‘Yan Sanda A Gombe Sun Kama Barayin Shanu Tsaro
Sarkin Gombe Yayin Hawan Tudun Wada Labarai
Shahararren Dan Dambe Anthony Joshua Yayi Hatsarin Mota A Jihar Ogun Labarai
Shin Ko Ganawar Zelensky Da Macron Zata Haifar Da ‘Da Mai Ido? Labarai
Shugaban Kasar Koriya Ta Arewa Ya Zamo Sakataren Jam’iya Mai Mulki Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Domin Inganta Tsaro Najeriya Ta Sayi Jiragen Yaki A Kasar Italiya Tsaro
  • Wasan Hamayya (Istanbul Derby) Fenerbahçe Da Galatasaray 1-1 Labarai
  • An Tura Rundunar Tsaron Sham Zuwa Kakarshin Ikon Kurdawa Labarai
  • Kyaftin Na Super Eagles Ya Yi Ritaya. Wasanni
  • Afirka Ta Kudu Ta Kama ‘Yan ƙasar Kenya Su Bakwai Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Amurka Ta Kama Tsohon Ministan Kudin Kasar Ghana Afrika
  • Yan Fashi Sun Shiga Gidan Alex Iwobi A Ingila Wasanni
  • Burkina Faso Ta Sako ‘Yan Najeriya 11 Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.