Magoya Bayan Ƙungiyar Kwallon Kafa ta Nice, Sunkai Hari Wa ‘Yan Wasansu.
Dan wasan gaba na Najeriya Terem Moffi da abokin wasansa na Ivory Coast Jérémie Boga sun fuskanci mummunan hari daga magoya bayan OGC Nice da suka fusata a ranar Lahadi da yamma bayan rashin nasarar da kungiyar ta samu a hannun Lorient da ci 3-1 a wasan mako na 14 na gasar Ligue 1,
Lamarin mai ban mamaki ya faru ne a wajen cibiyar horar da ‘yan wasan bayan da kungiyar ta dawo daga wasan waje.
A cewar rahotanni, an naushi Moffi a jiki da kuma kugu, an tofa masa yawu a kai, sannan aka yi masa cin zarafin wariyar launin fata, wanda hakan ya sa ‘yan wasan biyu suka fara shari’a kan wadanda suke da hanu cikin faruwar abun.
Harin ya nuna karuwar tashin hankali tsakanin kungiyar da magoya bayanta, tare da takaicin da ke ta’azzara sakamakon rashin kyawun sakamako.
A ranar Litinin da yamma, ƙungiyar Nice ta fitar da wata sanarwa a hukumance mai karfi tana Allah wadai da lamarin yayin da take nuna goyon baya ga ‘yan wasan da aka kai wa hari.


