A kalla mutane 12 suka rasa rayukan su, yayin da kuma aka yi garkuwa da wasu 3, lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki wajen hakar ma’adanai a kauyen Atoso da ke jihar filato a Nijeriya, a cewar wani wakilin cikin gida ranar Laraba.

Daylop Solomon Mwantiri, wanda shi ne shugaban kungiyar matasan Berom, na Berom Youth Moulders Association (BYM), ya ce maharan, wanda ‘yan gari suka ce Fulani ne, dauke da makamai, sun kai farmakin ne a Daren Talata, inda suka jikkata karin wasu mutane biyar, da a yanzu ke kwance a Gadon asibiti da raunukan harsashin bindiga.
Wannan hari na baya bayannan nan, ya kara kunnan wutar rashin zaman lafiya da ake ta fama da shi a filato, yankin Nijeriya ta tsakiya inda yawan rigingimu na kabilanci da addini ke ta’azzara fada tsakanin manoma da makiyaya kuma ana ci gaba da samun barkewar rikici, duk da alwashin da gwamnati ta dauka na kawo zaman lafiya.
Mwantiri ya ce, harin da aka kai ranar Talata, ya biyo kwanaki kadan bayan hallaka wasu yara hudu a wani kauyen dake makwaftaka da Atoso, inda ya ke zargin hukumomi da nuna halin ko in kula.
Kungiyar ta BMY ta bukaci gwamnati da ta Aike da dakaru don su hana kiwon dabbobi a gonaki, kuma su kubuto da mutanen da aka sace.


