Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • REAL MADRID: VALVERDE YA SAMU RAUNI MAI TSANANI A ƘAFA Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • NIHSA Ta Yi Gargadin Ambaliyar Ruwa A Jihohi 15 Afrika
  • Gidauniyar Misilli Ta Tallafa Wa Yara Da Dattawa A Gombe Afrika
  • Laccar Bagauda Kaltho Ta Jaddada Muhimmancin Yaƙi Da Yaɗa Labaran Karya Afrika
  • Cutar Mashako: Gwamnatin Gombe Ta Fara Rigakafin Gaggawa A Makarantu Kiwon Lafiya

Mali Da Burkina Faso Za Su Haramta Wa Amurkawa Izinin Shiga Ƙasashen Su
Published: January 1, 2026 at 10:44 AM | By: Bala Hassan

Kasashen Mali da Burkina Faso sunce za su hana Amurkawa izinin shiga kasashen su, martani kan irin wannnan matakai da gwamnatin Trump ta bada sanarwa akai a farkon watan Disemban 2025.

A cikin sanarwar da ma’aikatun harkokin kasashen wajen biyu suka bayar daban-daban a daren  litinin, kasashen biyu da suke Afirka ta yamma sunce suna daukar wannan matakine a zaman “martani” bayanda fadar White House ta bada sanarwar ranar 16 ga watan disemba cewa shugaban Amurka Donald Trump, zai kara kasashen su da wasu biyar a jerin kasashen da Amurka zata iya haramtawa shiga kasar.

Fadar White House tace jerin kasashen da matakin zai shafa zai fara aiki daga  1 ga watan Janairu na sabuwar shekara, ya shafi kasashe da suka ci gaba nuna rashin tantan-cewa na kwarai, yin kididdiga, da kuma musayar bayanai domin kare Amurka ta fuskar tsaro da kuma barazana kan zaman lafiya.

Mali ta fada a talata cewa shawarar da hukumomi a Washington suka dauka na sanya kasar cikin jerin kasashen da zata haramtawa shiga, ta yi hakan ne ba taredaa wata tuntuba ba, kuma hujjar data bayar na yin haka yayi karo da hakikanin al’amura.

Kasashen Mali da Burkina Faso ba sune kasashe na farko da suka dauki irin wannan mataki da ya shafi Amurkawa ba, bayan gwamnatin Trump ta auna su da irin wannan mataki.

Ranar 25 ga watan  Disemba da ta wuce kasar Nijar makwabciyar wadannan kasashe ta bada sanarwar cewa zata daina bada Visa ga Amurkawa, kamar yadda kafofin yada labaran kasar suka fada, daga bakin masana harkokin difilomasiyyar kasar.

A cikin watan Yuni ne kasar Chadi ta bada sanarwar dakatar da bada visa ga Amurkawa, bayan da gwamnatin Amurkan ta saka kasar a jerin kasashe 12 da haramcinta shafa.

 

Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Post navigation

Previous Post: Tinubu Yace Zayyi Hadaka Da Kasashen Duniya Domin Kawo Karshen Rashin Tsaro.
Next Post: Jamhuriyar Congo Zata Cigaba Da Fitar Da Ma’adanai

Karin Labarai Masu Alaka

An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara Afrika
Putin, Sakon Sabuwar Shekara Ya Jinjinawa Dakarun Rasha Da Suke Yaki A Ukraine Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Tantance Gaskiyar Bayanai Shi Ne Ginshiƙin Aikin Jarida Mai Nagarta – Abdulaziz Afrika
Pantami Ya Bayyana Dalilin Mayar Da Zaben Sa Abuja Afrika
Manoma Da Makiyaya: An Bukaci A Gaggauta Tantance Hanyoyin Shanu Da Iyakoki A Dukku Afrika
Shugaba Tinubu Ya Gana Da Wasu Gwamnoni Shida Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • REAL MADRID: VALVERDE YA SAMU RAUNI MAI TSANANI A ƘAFA
  • NIHSA Ta Yi Gargadin Ambaliyar Ruwa A Jihohi 15
  • Gidauniyar Misilli Ta Tallafa Wa Yara Da Dattawa A Gombe
  • Laccar Bagauda Kaltho Ta Jaddada Muhimmancin Yaƙi Da Yaɗa Labaran Karya
  • Cutar Mashako: Gwamnatin Gombe Ta Fara Rigakafin Gaggawa A Makarantu

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Sojin Najeriya Da Amurka Sun Hallaka Jagoran ISIS Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Na Shirin Yin Zamiya Don Biyan Bashi Labarai
  • Amurkawa Suna Turuwa Zuwa Kasar Faransa Duk Da Rashin Jituwa A Tsakanin Kasashen Amurka
  • Kwamitin Aikin Hajjin Najeriya Ya Shigar Da Korafi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane A Kauyuka Dake Yammacin A Najeriya Najeriya
  • Domin Inganta Tsaro Najeriya Ta Sayi Jiragen Yaki A Kasar Italiya Tsaro
  • Mace Ta Farko Da Zata Shugabanci Jami’ar Northwest Dake Kano Najeriya
  • Malami: Gwamnatin APC Ta Gaza – “Yan-Kasa Kuwa Na Da Katin Zabe” Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.