Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Mataimakin Shugaban Kasar Amurka Ya Gana Da Wasu Wakilai
Published: April 2, 2026 at 9:02 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Mataimakin Shugaban Amurka JD Vance ya yi mu’amala da wasu wakilai ta hanyar masu shiga tsakani daga ƙasar Pakistan game da rikicin Iran har zuwa ranar Talata, a cewar wani mutum da ke da masaniya game da lamarin wanda ya shaida wa Reuters. Wannan na nuna yadda rawarsa ke ƙara faɗaɗa wajen ƙoƙarin samar da mafita don kawo ƙarshen rikicin.

Bisa umarnin Shugaba Donald Trump, Vance ya aika da saƙo a ɓoye cewa Trump yana buɗe ƙofa ga tsagaita wuta muddin an cika wasu buƙatun Amurka, kamar yadda majiyar ta shaida wa Reuters a ranar Laraba.

Haka kuma Vance ya isar da abin da majiyar ta bayyana a matsayin “saƙo mai tsauri,” inda ya nuna cewa Trump ya fara gajiya da jinkiri, tare da gargadin cewa za a ƙara matsa lamba kan muhimman ababen more rayuwa na Iran idan Tehran ba ta amince da yarjejeniyar ba.

Majiyar ta ƙara da cewa ƙasar Pakistan na taka rawa a matsayin mai shiga tsakani tsakanin Amurka da Iran.

Vance na taka muhimiyar rawa wajen ƙoƙarin tattaunawa domin kawo ƙarshen yaƙin, wanda yanzu ya shiga mako na biyar.

Ana kallon sa a matsayin wanda zai iya gadan Trump a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2028, kuma ya ɗauki matakin taka-tsantsan game da rikicin, wanda ya dace da ra’ayinsa na dogon lokaci na nuna shakku kan tsawaita shiga harkokin sojan Amurka a ƙasashen waje.

Amurka, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Amurka Zata Fice Daga Iran Cikin Gaggawa
Next Post: Sojojin Isra’ila Sun Kashe Babban Kwamandan Kungiyar Hezbollah

Karin Labarai Masu Alaka

‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 30 A Jihar Neja Najeriya
Shugaba Trump Yace Amurka Ce Zata Rika Gudanar Da Harkokin Kasar Venezuela Amurka
Ambaliyar Ruwan Sama Yayi Ajalin Mutum 13 A Malawi Labarai
Shugaban Amurka Ya Ya Bukaci Iran Ta Mika Wuya Afrika
Netanyahu: Zamu Kashe Dala Billiyan $110 Cikin Shekaru Hudu Don Kera Makamai Sauran Duniya
Shugaba Trump Ya Hana Kaiwa Cuba Man Fetur Daga Venezuela Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Jihar Gombe Tayi Fice A Bangaren Inganta Lafiya Matakin Farko Najeriya
  • Jirage Marasa Matuka Sun Kaiwa Jiragen Ruwan Mai Hari A Gulf Afrika
  • EFCC Ta Tsare Tsohon Minista Abubakar Malami Tsaro
  • Shugaban Kasar Ivory Coast Yayi Sauye-Sauye A Majalisar Ministocin Kasar Siyasa
  • Kasar China Ta Kaddamar Da Rawar Daji A Yankin Taiwan Labarai
  • Arteta, Arsenal Zata Yi Sauye-Sauye A Janairu, Wasanni
  • Majalisar Dattawan Amurka Ta Amince Da Wata Doka Amurka
  • Kasar Uganda Ta Tsare ‘Yan Jam’iyyun Adawa Dubu Biyu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.