Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Mayakan Houthi Zasu Shiga Yakin Amurka Da Isra’ila
Published: March 28, 2026 at 10:24 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Kungiyar mayakan Houthi a Yemen mai samun goyon bayan Iran ta fada jiya jumma’a cewa, a shirye take ta fada yakin hadin guiwar da Amurka da Isra’ila suka kaddamar kan Iran idan wasu kasashe suka shiga yakin a gefen Amurka da Isra’ila, ko kuma idan aka yi amfani da bahar maliya wajen kaddamar da hari kan jamhuriyar Farisan mai bin tafarkin Islama, kamar yadda kakakin kungiyar mayakan sakan Yahya Saree, ya fada ta gidan talabijin.

Saree, yace a shirye kungiyar take ta shiga yakin, muddin aka ci gaba da zafafa hare hare kan Iran da kuma wadanda ya kira “murhun kare kai,” sai dai bai fayyace ta irin yadda za su shiga yakin da ake yi ba.

Gargadin da kungiyar ta Houthi tayi, yana kara nuna yadda yakin zai iya ba zuwa ya shafi yankin duka, musamman ganin karfin kungiyar na kai farmaki nesa daga Yemen, da kuma kassara zirga zirga a ruwayen da suke yankin na zirin Arabaiya.

Tuni kawayen Iran ‘yan shi’a a Lebanon da Iraqi suka shiga yakin da ake yi a yankin, sakamakon harin da Amurka da Isra’ila suka auna kan Iran.

Afrika, Amurka, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Ministan Harkokin Wajen Rasha Dana Iran Sun Tattauna Don Kawo Karshen Yaki A Gabas Ta Tsakiya
Next Post: China Da Jamhuriyar Dimokraɗiyya Kwango Sun Kulla Yarjejeniya

Karin Labarai Masu Alaka

Shirin Kwace Iyakar Greenland Da Shugaba Trump Yakeyi Yabawa Kasashen Turai Mamaki Amurka
Iran Da Amurka Zasu Cimma Yarjejeniyar Nukiliya Amurka
Gwamnan Jihar Kebbi Ya Amince Da Biyan Hakkokin Tsofin Ma’aikata 800 Labarai
Kotu A Kasar Faransa Ta Daure Roger Lumbala Shekaru 30 Labarai
Guinea Bissau Ta Tsaida Gwaje-Gwajen Allurar Rigakafin Shawara A Kasar Labarai
Bayan Ya Ziyarci Kwankwaso Gawuna Zai Karbi Katin ADC Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Kasar Amurka Da Rasha Zasu Kawo Karshen Tsagaita Nukiliya Amurka
  • Hamas Ta Kwance Damara Afrika
  • Kungiyar MDD Ta Bukaci Ayi Bincike Game Da Kashe ‘Yan Iran Sauran Duniya
  • Dubban ‘Yan Gudun Hijira Sun Halaka Amurka
  • Gwamnatin Najeriya Tace Ta Farmaki Mayakan ISIS A Jihar Sokoto Labarai
  • Rundunar Sojin Najeriya Ta Dakile Harin ‘Yan Ta’adda A Jihar Borno Labarai
  • Matatar Man Dangote Zata Bada Kwangilar Sayar Da Gas Da Man Jirage Afrika
  • Tinubu Ya Bayyana ‘Yan Bindiga Da Cewa Ruwa Yakarewa Dan Kada Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.