Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Mutane 13 Sun Mutu Inda Wasu 57 Suka Jikkata A Barundi
Published: April 2, 2026 at 1:25 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Mutane goma sha uku sun mutu, yayin da wasu 57 suka jikkata sakamakon fashewar wasu ababe fashewa sanadiyyar matsalar wutar lantarki a wani sansanin sojoji na ƙasar Burundi a daren Talata, kamar yadda rundunar sojin ƙasar ta bayyana.

Mai magana da yawun sojojin Burundi, Gaspard Baratuza, ya shaida wa taron manema labarai a jiya Laraba cewa gidaje, gine-gine, motoci da kayan aikin soja sun lalace a sakamakon fashewar rumbun ajiyar makamai a Bujumbura, cibiyar kasuwancin ƙasar.

Wani mazaunin Bujumbura da ke zaune kusa da wurin yace fashe-fashen sun ɗauki sa’o’i da dama suna ci gaba.

Ya ce, “An shafe kusan sa’o’i shida ana ganin harsasai suna shawagi a sama suna sauka a wurare daban-daban.” Ya ƙara da cewa, “Mun dai tsaya a inda muke muna fakewa domin tsira,” kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters, inda ya nemi a sakaya sunansa.

A unguwar Musaga da ke kusa da sansanin sojin, wani mazauni ya ce ya ga wata budurwa ta faɗi ƙasa yayin da take gudu tare da wasu mutane. “Bayan ɗan lokaci ne na fahimci cewa bam ya bugi jikin ta da ƙarfi,” in ji shi, shi ma ya nemi a ɓoye sunansa.

Wani mutum kuma ya mutu jim kaɗan bayan an kammala taron addu’a a wata coci a unguwar Gasekebuye, kamar yadda wani mazaunin yankin ya bayyana.

Afrika, Labarai, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Farashin Mai Ya Ragu A Kasuwar Duniya
Next Post: Domin Karfafa Tsaro Babban Hafsan Sojin Najeriya Ya Ziyarci Jos

Karin Labarai Masu Alaka

Shugaban Ƙasar China Zai Karbi Bakwancin Shugaban Koriya Ta Kudu Afrika
Kungiyar Cigaban Al’ummar Tangale Tace Bata Goyon Bayan Kai Ziyara Wa Gwamnan Gombe Labarai
Ghana Ta Haramta Hakar Ma’adinai A Gandunan Dajin Data Kebe, Labarai
Ana Cigaba Da Ceto Masunta Daga Ruwa A Ghana Labarai
An Kaddamar Da Rigakafin Cutar HIV AIDS A Kasar Zimbabwe Kimiya
Wasan Hamayya (Istanbul Derby) Fenerbahçe Da Galatasaray 1-1 Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Majami’ar Anglican Zasuyi Taron Zaben Sabon Shugaba Afrika
  • Kudin Man Fetur Ya Karu Da Kashi 10 Cikin 100 Afrika
  • Sabon Jagoran Addinin Iran Mojtaba Khameni Yaji Rauni Kuma Ya Nakasa Afrika
  • Hukumar Zabe A Najeriya Ta Cigaba Da Rijistar Katin Zabe Labarai
  • Shugaban Kasar Iran Yace Kasar Bata Da Kiyayya Tsakaninta Da Amurkawa Afrika
  • Najeriya Na ƙoƙarin Shiga Gasar Cin Kofin Duniya 2026 Ta Barauniyar Hanya Wasanni
  • Wata Tankar Mai Ta Kife A Apapa Legas Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • An Dakatar Da Daniel Bisa Zargin Fyade Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.