Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnan Gombe Yace An Sace Yara 48 A Jihar Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • ‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Netanyahu: Zamu Kashe Dala Billiyan $110 Cikin Shekaru Hudu Don Kera Makamai
Published: December 25, 2025 at 7:12 AM | By: Bala Hassan | Updated: December 25, 2025

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a laraba yace kasar bani yahudun, zata kashe kudi dala bilyan 110 cikin shekaru hudu masu zuwa, wajen kafa sashen kera makamai maizaman kansa domin kasar ta rage dogaro kan wasu kasashe wajen samun makamai.

“Zamu ci gaba da neman wasu muhimman bukatu, a hanu daya kuma zamu samar da makamai da kan mu, inji PM Netanyahu a lokacinda yake magana a bikin kaddamar da shirin.

Bana cewa kasa zata iya biyawa kanta bukatunta kachokam ba, amma zamu yi bakin kokarin mu waje ganin haka. “in ji shi.

Burin mu shine gina sashen kera makamai na kasar Isara’ila domin mu rage dogaro kan kasashe ciki harda kawayen mu.

A gefe daya kuma, Isra’ila ta fada a Laraban nan cewa, zata dauki fansa bayan da ta zargi Hamas da keta yarjejeniyar tsagaita wuta, bayanda wani sojanta ya sami rauni sakamakon wata fashewa a Gaza, sai dai hamas ta musanta zargin, tana mai cewa, fashewar daga wani makami ne da aka bari a wurin tun lokacinda ake bata kashi.

PM Netinyahu ya ma baci lamarin ne da ya auku a Rafah, inda Isra’ilan take daukar matakan soji a yayinda yake magana a wani bikin yaye daliban makarantar horasda sojojin sama na kasar, ya kara da cewa Hamas ta fito fili ta nuna cewa ba zata kwance damara ba, kamar yadda yake kunshe cikin yarjejeniyar da aka kulla na tsagaita wuta  a cikin watan Oktoba.

A wani gefe kuma, yan share wuri zauna na Isra’ila a wani dan karamin wuri da ake kira Or Meir, sun bayyana a shafukan Telegram shirin su na ci gaba da korar Falasdinawa a yankin.

Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Zelensky Na Buƙatar Ganawa Da Trump Domin Cimma Matsaya Kan Batutuwa Masu Sarƙaƙiya
Next Post: Amurka Ta Sanya Hanu Kan Yarjejeniyar Kiwon Lafiya Da Ƙasashen Madagascar, Saliyo, Botswana, Ethiopia

Karin Labarai Masu Alaka

An Kaddamar Da Rigakafin Cutar HIV AIDS A Kasar Zimbabwe Kimiya
Ana Jimamin Mutuwar Giwa Mai Shekaru Kusan 60 A Kasar Kenya Sauran Duniya
Sanarwar MDD Ya Nuna Aniyar Mayakan RSF Na Kisan Kare Dangi Afrika
Masu Goyon Bayan Palasdinawa Sunyi Gangamin Zanga Zanga A Australia Labarai
Guinea Bissau Ta Tsaida Gwaje-Gwajen Allurar Rigakafin Shawara A Kasar Labarai
Shugaban Kasar Iran Ya Bayyana Samun Sakamako Mai Kyau A Tattaunawa Da Amurka Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ‘Yan Uwa Musulmi A Jihar Gombe Sunyi Allah Wadai Da Kisan Ayatollah Khomeini
  • An Samu Kaburbura Biyu Dauke Da Gawarwaki 173 A Kasar Kwango
  • Yan Bindiga Suna Cigaba Da Kashe Mutane A Garin Gwana Dake Jihar Bauchi
  • Karancin Iskar Gas Kalubale Ne Ga Wutar Lantarki
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Hukumar Zabe A Kasar Honduras Ta Sanar Da Nasry Asfura A Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben Shugaban Ƙasa Afrika
  • Channels TV: Ta Yi Rashin Hazikin Dan Jarida Mr Khani Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Shugaban Kasar Koriya Ta Arewa Ya Zamo Sakataren Jam’iya Mai Mulki Labarai
  • An Kubutar Da ‘Yan Matan Sakandire Su 24 Na Jihar Kebbi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Shugaban Koriya Ta Arewa Ya Gabatar Da Gwajin Makami Mai Linzami Afrika
  • Ana Cigaba Da Samun Hare Hare Da Jiragen Marasa Matuki A Sudan Labarai
  • Amurka Ta Daina Bawa Israila Bayanan Sirri Amurka
  • Asusun IMF Zai Bawa Kasar Misra Lamunin Sama Da Dala Biliyan 2 Sauran Duniya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.