Rikicin Iran: Farashin Litar Man Fetur Ya Zama Naira 1,400 A Maiduguri
Daga Adamu Aliyu Ngulde a Maiduguri Jihar Borno.
Sakamakon hare-haren da ke ƙara ta’azzara tsakanin ƙasashen Iran da Amurka da kuma Isra’ila, wasu mazauna birnin Maiduguri, na jihar Borno sun fara ji a jika, domin kuwa tashin farashin man fetur ya fara shafar tattalin arzikin marasa galihu.
Wakilin GTA Hausa, a birnin Maiduguri, Adamu Aliyu Ngulde, na ɗauke da ƙarin bayani cikin rahoton da ya aiko mana.


