Rundunar Tsaron haɗin gwiwa ta Arewa maso Gabashin Najeriya, Operation Hadin Kai (OPHK), ta kashe ‘yan ta’adda 438 na Boko Haram da ISWAP cikin watanni bakwai.
Kwamandan rundunar OPHK a yankin Arewa maso Gabas, Sashi na daya, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, ne ya bayyana hakan a ranar Asabar yayin liyafar Kirsimeti da aka gudanar a Maiduguri, inda ya ce an gudanar da ayyukan ne tsakanin watan Mayu da Disamba.
Abubakar ya ce jami’an rundunar sun kuma ƙwato makamai iri-iri 254, na’urorin sadarwa na Starlink guda 300, tare da ceto fararen hula 366 daga maboyar ‘yan ta’adda daban-daban.
Ya ce, Mika wuya da ‘yan ta’adda 881 na JAS/ISWAP tare da iyalan su, na daga cikin manyan nasarorin da suka nuna ci gaban da aka samu.
Janar ɗin sojan ya ƙara da cewa bikin Kirsimeti ya zo dai dai da ayyukan rundunar na lokacin rani a yankin.
Abubakar ya danganta nasarorin da aka samu a ayyukan haɗin gwiwar bisa ga samun goyon baya daga Babban Hafsan Sojojin Ƙasan Najeriya.


