Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa Afrika
  • Gwamnan Jihar Bauchi Ya Jagoranci Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Rangadi A Bauchi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Amince Da Naɗin Manyan Sakatarori 19 Afrika

Sabuwar Shekarar Musulunci: Shugaban Gwamnonin Arewa Ya Yi Kira Da A Yawaita Addu’o’i Da Haɗin Kai
Published: June 16, 2026 at 9:40 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnan jihar Gombe kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF), Muhammadu Inuwa Yahaya, ya taya al’ummar Musulmi a Jihar Gombe da Najeriya baki ɗaya, har ma da sauran Musulmi a faɗin duniya, murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1448 Bayan Hijira (AH).

A cikin saƙon taya murna da ya fitar domin bikin sabuwar shekarar Hijira, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana farkon sabuwar shekarar Hijira a matsayin lokaci na sabunta ruhi, yin nazari mai zurfi kan rayuwa da kuma ƙara jajircewa wajen bin koyarwar addini, zaman lafiya, tausayi da yi wa bil’adama hidima.

Gwamnan ya ce sabuwar shekarar Musulunci wata dama ce ga al’ummar Musulmi domin su yi waiwaye kan abubuwan da suka gabata, su ɗauki darussa daga gare su sannan su fuskanci gaba da ƙarin imani, fata da ƙuduri.

Ya ce, “Yayin da muke shiga sabuwar shekarar Hijira, ya kamata mu ƙara rungumar kyawawan ɗabi’u na haƙuri, sadaukarwa, juriya da adalci waɗanda Ma’aiki Mai Tsira Annabi Muhammad (SAW) ya nuna a lokacin Hijira.”

Gwamna Inuwa Yahaya ya buƙaci Musulmi da su yi amfani da wannan wata mai alfarma na Muharram da sauran watannin da ke gaba wajen ƙara yawaita addu’o’i domin samun ɗorewar zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba a Jihar Gombe da Najeriya baki ɗaya.

Har ila yau, ya yi kira da a yi addu’o’i na musamman domin samun wadataccen ruwan sama da kuma nasarar kakar noma, yana mai bayyana fatan cewa sabuwar shekarar za ta zo da ƙarin ci gaba da damammaki ga al’umma.

Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa ya kuma jaddada muhimmancin zaman lafiya tsakanin al’umma, girmama juna da haɗin kai tsakanin kabilu da addinai daban-daban a jihar da ƙasa baki ɗaya, musamman a wannan lokaci da ake fuskantar ƙalubalen tsaro a wasu sassan ƙasar.

Gwamna Inuwa Yahaya ya sake tabbatar da aniyar gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da manufofi da ayyukan raya ƙasa da ke da tasiri kai tsaye ga rayuwar jama’a domin inganta walwala da yanayin rayuwarsu.

Ya kuma buƙaci al’umma da su kasance masu bin doka, masu tsayawa kan koyarwar addini da kuma jajircewa wajen gina al’umma mai zaman lafiya, tsaro da ci gaba.

A ƙarshe, Gwamnan ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da Ya sanya sabuwar shekarar Musulunci ta kasance mai cike da zaman lafiya, ci gaba da rahama ga jihar Gombe, Arewacin Najeriya da ƙasar baki ɗaya.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: EU Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Amurka Da Iran
Next Post: Sabuwar Shekarar Musulunci 1448: Kiristoci Sun Yi Murna, Sunyi Kiran Samar Da Hutu Ga Shekarar Musulunci

Karin Labarai Masu Alaka

Tsohon Jagoran Masu Kishin Kasa A Hungry Ya Amince Da Shan Kaye Labarai
Jihar Gombe Ta Karbi Bakuncin Taron Tsaro Tsakanin DIG Da Masu Ruwa Da Tsaki Afrika
‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 30 A Jihar Neja Najeriya
Kasashen Yankin Gulf Sun Bukaci Amurka Takawo Karshen Iran Afrika
APC Ta Bayyana Abba Yusuf A Matsayin Halastaccen Ɗan Takara Bayan Cika Sharudda Afrika
Harin Jirgi Marar Matuki Ya Kashe Kakakin ‘Yan Tawayen M23 Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Sojoji Sun Ceto Mutane 23, Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 19 A Cikin Sa’o’i 24
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe
  • Builder Mahmood Yusuf Ya Tallafa Wa Mata Da Matasa
  • Trump Ya Yi Gargadi Kan Shirin Cire Shugaban FIFA Infantino
  • Katsina United Ta Yi Jimamin Mutuwar Ɗan Wasanta Ozoh

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Akwai Bukatar APC Tayi Gyare-Gyare Kafun Zabe Afrika
  • Gwamnonin Arewa Sun Kaddamar da Kwamitin Asusun Tsaro Afrika
  • Shugaba Bola Tinubu Ya Tafi Turai Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Shugabar Hamayya A Venezuela Ta Gana Da Paparoma Leo Amurka
  • Amurka Tace Zata Gama Yakin Iran Cikin Makonni Afrika
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran Amurka
  • GTA Hausa Logo
    Shirin Dare 2030 UTC Yau Juma’a 11.21.2025 Rediyo
  • Shugaba Tinubu Ya Gana Da Masu Zuba Jari A Birnin Paris Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.