Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maikaba Ya Yi Murabus A Matsayinsa Kocin Wikki Tourist FC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • NEDC : Zata Samar Da Cikekken Kulawa Wa ‘Yan Jaridar Da Sukayi Hatsari A Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Trump Zata Kafa Kasuwar Ma’adanai Amurka
  • An Yanke Mishi Hukuncin Kisa Saboda Neman Kudin Aure Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Babban Malamin Musulunci Sheikh Usman Kusfa Zaria Ya Rasu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Shugaba Donald Trump Ya Nada Shugaban Bankin Tarayya
Published: January 30, 2026 at 10:28 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da nada Kevin Warsh a matsayin shugaban bankin tarayya na kasa don maye gurbin Jerome Powell, wanda wa’adin sa zai kare ranar 15 ga watan Mayu. Tun Jiya rade-radin nada Warsh din ya dagulawa kasuwannin hannun jari lissafi, inda farashin gwal ya fadi da fiye da kashi hudu cikin 100 saboda ganin da ake masa na me tsatssauran ra’ayi ne, amma duk da haka gwal din na daf da samun riba mafi tsoka cikin wata daya da bai taba samu ba tun shekarar 1980, bayan da masu sa hannun jari suka koma sayen sa a matsayin mafaka lokacin da ake tsaka da rigingimun siysar kasa da kasa, da kuma rikicin tattalin arziki.

Gwal da ake kira spot gold ya yi asarar kashi 3.9 cikin dari, yayin da kuma hada-hadar gwala-gwalan a kasuwar Amurka yayi asarar kashi 2.7 cikin dari.

Bayan gwal ma, farashin kayyaki a kasuwannin hannun jari sun yi kasa, duk saboda rade-radin cewa Kevin Warsh zai maye gurbin Jerome Powell.

Hannayen jari masu sauki na S&P 500 sun fadi da kashi 0.4 cikin dari, yayin da na Nasdaq suka fadi da kashi 0.5 cikin dari, farashin sauran duwatsu masu daraja suma suka fadi, bayan da kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ruwaito cewa Kevin Warsh ya ziyarci fadar White House don ganawa da Donald Trump ranar Alhamis.

Amurka, Labarai

Post navigation

Previous Post: Afirka Ta Kudu Ta Bukaci Jakadan Israela Ya Fice Daga Kasar
Next Post: Cutar Kurkunu Ta Kusa Zamowa Tarihi A Duniya

Karin Labarai Masu Alaka

Majalisar Dattawa Ta Amince Tinubu Ya Tura Sojoji Benin Labarai
Amurkawa Sun Nuna Bacin Rai Saboda Yawaita Kashe ‘Yan Kasar Amurka
Rasha Da Ukraine Sun Cigaba Da Yakar Juna Afrika
Shugaban Kasar Uganda Yana Kokarin Mayar Da Mulkin Kasar Na Gado Labarai
Gwamnan Jihar Gombe Ya Umurci A Rufe Makarantu Labarai
Mala Buni: Zai Jagoranci Kwamitin Sassanci Na Jam’iyar APC Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Muna Kokarin Kawo Karshen Cin Zarafin Jinsi A Gombe – Uwargidan Gwamna
  • Majalisar Dattawar Najeriya Ta Amince Da Tura Sakamakon Zabe Ta Intanet
  • Yeriman Ingila Ya Gana Da Yeriman Saudiya Mai Jiran Gado
  • Dubban Mutane Sunyi Zanga-Zanga A Kasar Australia
  • Bangladesh Tasamu Rangwamen Harajin Da Amurka Ta Kakaba Mata

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Sheikh Ibrahim Sheikh Dahiru Ya Zamo Khalifan Sheikh Dahiru Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Amurka Ta Gabatarwa Sassan Dake Yakar Juna A Sudan da Shirin Tsagaita Wuta Afrika
  • Jirgin Sojin Saman Najeriya Yayi Hatsari a Jihar Neja Labarai
  • Ana Cigaba Da Bincike Game Da Mutuwar Matar Da Likita Ya Manta Almakashi A Cikinta A Kano Najeriya
  • Matatar Man Dangote Ta Samu Tagomashi Daga Abokan Hulda Najeriya
  • ‘Yan Agajin Izalar Jos Sunyi Hatsari Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Jirgin Sama Ya Fadi A Kano Labarai
  • Yau Litinin Za’a Mika Daliban Ga Iyayen Su Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.