Magoya bayan shugaba Kais Saied na Tunisia sun yi gangami a babban birnin kasar ranar Laraba, inda suke kiran ‘yan adawa da maciya amana, biyo bayan zanga-zanga da aka yi ta yi a tituna a makonnin baya bayannan da ke nuni da karin tsami a banbance banbancen siyasa.
Wannan gangami na ‘yan adawar siyasa, ya zo lokacin da ake tsaka da matsalar tattalin arziki da ya haifar da hauhawar farashi, karancin wasu kayayyakin bukatun yau da kullum da kuma rashin ingancin gwamnati, abin da ya haifar da fushin al’umma.
Kungiyoyin kare hakki sun zargi shugaba Saied da yiwa ‘yan adawa karfa-karfa, inda suka ce yana amfani da kotuna da ‘yan sanda don rufe bakin su amma Saed ya karyata Wannan Zargi, inda ya ce yana tsaftace kasar ne daga maciya amana, da kuma gurbatattun manyan mutane.
Masu zanga-zangar sun taru a birnin Tunis suna daga tutocin kasar, suna rera taken goyon baya ga Saied, wanda suke cewa kokarin magance almundahana da kuma gurbattatun manyan ‘yan siyasa.
Sun Zargi ‘yan adawa da neman kawo hargitsi a kasar, inda suka ce maciya amana ne kuma Suna cewa mutane Saeid suke so, muna bin goyon bayan shugabanci da mulkin sa.


