Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Shugaban Amurka Donald Trump Yace Amurka Zata Kai Babban Farmaki Iran
Published: March 14, 2026 at 4:15 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Shugaba Donald Trump yace Amurka zata kai farmaki mai tsanani kan Iran “makon da yake zuwa,” jim kadan bayan da ya dage takunkumi kan sayen mai daga Rasha na tsawon kwanaki 30, da nufin saukaka farashin mai da yayi tashin goron zabbi, sakamakon hare-haren hadin guiwar da Amurka da Isra’ila suka kaddamr kan Iran.

Farashin mai yana kwan gaba kon baya kan canjin kalaman shugaba Trump game da tsawon lokaci da zai dauka a kammala wannan yaki, wadda yasa Iran take kai hare hare kan jiragen ruwa a mashigin ruwan Hormuz, hanyar da ake bi da kashi 1 cikin biyar na mai da duniya take amfani dashi.

A baya shugaba Trump yace “an gama yakin,” ya kuma yi alkawarin baiwa jiragen ruwan kariya a mashigin ruwan Hormuz. A hira da yayi da tashar talabijin ta FOX da tashar ta nuna jumma’an nan , Trump yace Amurka zata raka jiragen ruwan da za su bi ta mishigin ruwan “idan muka buka ci yin haka.”

Farashin mai da ake kira Brent ya sauka zuwa dala 99. da centi 80, wadda har yanzu yake nuna farashin man ya karu da kamar kashi 40 cikin dari tun fara wannan yaki.

Ahalinda ake ciki kuma jani-injaka ya turnuke a fadar White House tsakanin hadiman shugaba Trump ta hanyar da Amurka zata ayyana nasara a yaki kan Iran yayinda rikicin yake kara bazuwa a fadin gabas ta tsakiya, ganin babu wata mafita kai tsaye da Amurka zata bi ta tsaida fadan.

Afrika, Amurka, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Yunkurin Samar Da ‘Yan Sandan Jihohi Na Kara Kankama A Najeriya
Next Post: Gabannin Harin Amurka Da Isra’ila Iran Farisa Ta Shirya Nata

Karin Labarai Masu Alaka

Kotu A Kasar Faransa Ta Daure Lumbala Shekaru 30 Bisa Laifin Cin Zarafi Labarai
Sojojin Da Suka Kifar Da Farar Hula A Guinea-Bissau Sun Sanar Da Cewa! Afrika
Gwamnatin Najeriya Ta Dauki Matakai Don Farfaɗo Da Maɗaba’ar Gwamnati Labarai
Akwai Alamar Shawarwari Tsakanin Amurka Da Turai Zai Kawo Karshen Yakin Rasha Amurka
Gwamnatin Bauchi: Ta Kaddamar Da Kwamitin Ma’adanai Labarai
An Yi Fashin Kaguwa Da Dodon-Kodi Na Miliyoyin Dalar Amurka Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Ethiopia Tana Horas Da Dakarun RSF A Wani Sansani Afrika
  • Pakistan Da Afghanistan Sun Shiga Kwana Na Biyar Suna Fafatawa Afrika
  • An Kubutar Da ‘Yan Matan Sakandire Su 24 Na Jihar Kebbi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Amurka Na Kokarin Watsi Da Tsohuwar Dokar Jones Labarai
  • Ahmed Musa, Yayi Ritaya A ƙwallon ƙasa Da ƙasa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Kasar Spain Zata Bada Diyya Ga Iyalen Wadanda Da Suka Rasu A Hatsarin Jirgin Kasa Labarai
  • Farashin Mai Ya Tashi A Kasuwannin Duniya Labarai
  • Amurka Zata Saidawa Saudiyya Da Jirgin Yaki Samfurin F35 Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.