Wani gungun shugabannin darikar Anglican ranar Alhamis suka bada sanarwar kafa wata sabuwar majalisa da zata jagoranci darikar, mataki da yake kalubale ga Arcbishop ta Cntebury, a dai dai lokacin da ake shirin bikin mika mata ragamar shugabancin darikar.
Wannan mataki da bangaren darikar da ake kira GAFCON a takaice, wato Globa Anglican Future conference da turanci, ya hada kan coci-cocin Anglican masu ra’ayin mazan jiya- galibi daga Asiya da Afrika, yana haska wuta kan kara zurfin sabani tsakanin ‘yan darikar bayan da aka shafe shekaru ana zaman dar dar kan akida da kuma batutuwa na zaman takewa.
Reshen cocin masu kiran kan su GAFCON a takaice, suna adawa kan nada mata a zaman limamai, da kuma kara cusa ‘yan luwadi da madugo cikin harkokin majami’ar.


