Sojin Isra’iala sun kashe a kalla Palasdinawa 2, ciki har da yarinya karama, sannan suka jiwa wasu hudu raunuka, suma cikin su akwai yara, a wani hari na jirgin sama da suka kai Khan Younis, a kudancin zirin Gaza ranar Litinin, a cewar jami’ai a Nasser, babban asibitin birnin.
Sojojin Isra’ila sun ce sun kai harin ne a wani wuri da ke karkashin ikon Hamas, kuma suna da zummar ya fada kan wani mayakin Hamas da ke shirin kai farmaki kan sojojin Isra’iala a kudancin Gaza.
Isra’iala ta ci gaba da kai hare-hare ta jiragen Gaza, tun bayan da Amurka ta jagoranci yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Octobar bara, Kasar Isra’ila ta ce tana kai hare-haren ne don dakile kai mata farmaki, da kuma lalata mata makamai.


