Binciken da rundunar sojin Nigeria ta yi ya gano akwai yiwuwar cewa wasu dakarun ta 16 da aka kama shekarar da ta gabata saboda aikata laifi, suna shirin kifar da gwamnati ne ta hanyar juyin mulki, kuma zasu fuskanci shari’a, a cewar wani jawabi da ya fito daga babban ofishin tsaro na kasa a ranar litinin.
Jawabin ya ce binciken da aka yi ya binciko sahihan abubuwa a kan da yawa daga cikin sojojin, ciki har da zargin shirin hambarar da gwamnati, amma bai bada bayanin yadda shirin nasu yake ba, da ko sojoji nawa daga cikin 16 ne ke da hannu ciki ba.
Mai magana da yawun hukumar tsaro major janar Samaila Uba, ya ce an tsare Jami’an sojojin a watan Octobar bara, wadanda kuma ake tuhumar su da laifin yunkurin Juyin mulki yanzu za’a tsayar da su gaban alkalin kotun soja. Ya kara da cewa, idan an kama su da laifi, zasu fuskanci hukuncin kisa.
A watan Octoba na shekarar da ta wuce ne, Shugaba Bola Tinubu ya sauya sojoji masu rike da manyan mukamai da wasu, a yunkurin sa na karfafa matakan tsaro, yayin da kasar ke fuskantar barazana daga kungiyoyin ‘yan ta’adda da dama.


