Ƙungiyar agajin gaggawa ta Falasɗinu (Palestinian Red Crescent) ta ce jami’an ceton gaggawa suna kula da mutanen da suka ji rauni sakamakon tarkacen makamai a yankin kogin Jordan da ake mamaye (West Bank) a daren jiya Laraba, yayin da Iran ke harba makamai masu linzami zuwa Isra’ila.
Ta ce wani hari ya kashe aƙalla mutane huɗu tare da jikkata wasu aƙalla shida a garin Beit Awa. Aƙalla mutane biyu daga cikin waɗanda suka ji rauni an kai su asibiti. Likitocin agajin gaggawa na Palestinian Red Crescent na ci gaba da tantance wadanda suka jikkata, kuma yawan waɗanda suka mutu ko suka jikkata na iya canzawa.
Wannan ne karo na farko da aka samu mace-mace a yankin West Bank da aka mamaye tun bayan fara yaƙin Iran. Tarkacen makamai masu linzami sun lalata gidaje da wuraren kasuwanci a cikin makonni biyu da rabi na farko.
Falasɗinawa ba su da isasshen tsarin mafaka da ƙararrawa (siren) kamar yadda Isra’ilawa ke da shi domin kare kansu daga makamai masu linzami masu shigowa ko tarkacensu daga Iran ko Hezbollah. Ba a tabbatar nan take ba ko mace-macen da raunin sun faru ne sakamakon harin kai tsaye ko tarkacen da ya faɗo bayan an dakile makaman.


