Shugaban Ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai bar Abuja ranar Talata domin kai ziyara ta ƙasa zuwa Kasar Burtaniya a matsayin baƙon King Charles III da Sarauniya Queen Camilla.
Sanarwar da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar ta ce Tinubu zai je tare da Uwargidan sa, Oluremi Tinubu, inda za a karɓe su a Windsor Castle daga 18 zuwa 19 ga Maris.
Rahoton ya ce wannan ita ce ziyara ta farko da shugaban Najeriya zai kai Birtaniya cikin shekaru 37, kuma za ta mayar da hankali kan ƙarfafa alaƙar ƙasashen biyu a fannoni kamar na kasuwanci, zuba jari, tsaro da musayar al’adu.
A yayin ziyarar, Tinubu zai kuma gana da Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, a 10 Downing Street, inda ake sa ran za a rattaba hannu kan yarjejeniyoyi da dama tsakanin ƙasashen biyu.
Ana sa ran Shugaban Ƙasar zai dawo Najeriya bayan kammala ziyarar.


