Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Togo Ta Kama Tsohon Shugaban Kasar Burkina Faso Saboda Kitsa Juyin Mulki
Published: January 20, 2026 at 8:09 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Togo ta kama tsohon shugaban kasar Burkina Faso, kuma ta tusa keyarsa zuwa kasar sa, bayan da jami’ai a Ouagadougou suka yi zargin yana kitsa juyin mulki, kamar yada wasu majiyoyi biyu suka fadawa kamfanin dillancin labarai na Reuters ranar talata.

Paul Henri Damiba, ya hau mulki ne a shekara ta 2022 sakamakon juyin mulki da sojoji suka yiwa gwamnatin farar hular kasar, wacce tayi bakin jini saboda yadda ‘yan tawaye masu ikirarin Islama suke tada kayar baya.

Sai dai shi ma Damiba, da ya kasa shawo kan fitinar ‘yan bindigar, lamarin ya harzuka dakarun kasar dake yammacin Afirka, shi ma aka yi masa juyin mulki a cikin shekarar da ya hau mulki, mataki da ya kawo shugabancin Ibrahim Traore, wanda yake ci gaba da mulkin kasar.

A farkon wannan wata, Burkina Faso tace ta wargaza wan yunkurin kashe Troare, da take zargin Damiba da kullawa, wanda yake zaman gudun hijra a Lome babban birnin kasar Togo.

Wata majiya ta fuskar tsaro, da wata majiya kusa da fadar shugaban kasar Togo, sun gayawa Reuters a ranar talata cewa, an kama Damiba, ranar Asabar, kuma an maida shi Burkina Faso.

A dai ranar Talatan gwamnatin kasar Togo ta tabbatar da wannan labari, kuma cikin sanarwar da ta bayar wacce aka rubuta ranar Litinin, sannan aka raba, Damiba, yana fuskantar zargin almubazzaranci da dukiyar al’umma, arzurta kansa ba bisa ka’ida ba, rashawa da kuma halatta kudaden haram, amma sanarwa bata ambaci zargin juyin mulki ba.

Kamfanin dillancn labarai na Reuters, ya kasa magana da Damiba, kuma babu tabbas ko yana da lauya a Togo. Gwamnatin Burkina Faso, bata maida martani ba da aka nemi jin ta bakinta.

Afrika, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo Ya Ziyarci IBB
Next Post: Sojojin Kasar Uganda Sun Bazama Neman Bobi Wine Sakamakon Rikicin Bayan Zabe

Karin Labarai Masu Alaka

Jagoran Kwankwasiya A Najeriya Ya Koma Jam’iyar ADC Labarai
Gwamnatin Sham Tace Harin Kurdawa Ya Hallaka Sojojin Kasar Afrika
Libya Ta Kulla Yarjejeniya Da Kasashen Faransa Da Amurka Afrika
Kasar Mauritius Zata Rage Amfani Da Makamashi Afrika
Dan Ra’ayin Mazan Jiya Leo Brent Zai Kyautata Alakar Afirka Ta Kudu Da Amurka Afrika
Harin Isra’ila A Gaza Da Jirgi Maras Matuki Ya Kashe Mutane Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • An Kusa Kawo Karshen Matsalolin Tsaro A Jihar Filato Afrika
  • Kungiyar ISIS Ta Kashe Sojojin Amurka Biyu Amurka
  • Shugaban Kasar Amurka Yakara Hana Wasu Kasashe Shiga Amurka Ciki Harda Nijar Amurka
  • Abun Da Kuke Buƙatar Sani Game Da Gasar Cin Kofin Ƙasashen Afirka 2025 Wasanni
  • Iran Ta Kai Hari Matatar Mai A Kuwait Afrika
  • Jamhuriyar Nijar Ta Fitar Da Doka Domin Kare ‘Yancin ‘Yan Kasar Tsaro
  • Jami’an Diflomasiyyar Iran Dana Amurka Sun Tattauna A Kasar Oman Afrika
  • ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Sojoji 15 Da Wasu Fararen Hula A Benin Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.