Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Amurka Ta Baiwa Najeriya Wasu Muhimman Kayan Yaki Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Trump Yayi Kira Ga ‘Yan Ƙasar Iran Su Ci Gaba Da Zanga Zanga Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Syria: Mutane Sun Yi Zanga Zanga Domin Nuna Rashin Amincewa Da Korar Kurdawa A Birnin Aleppo Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Trump Da Bin Salman Da Wasu Kasashe Za Su Sa Hannu A Rikicin Sudan
Published: November 20, 2025 at 2:40 PM | By: Yusuf Aliyu Harande

Shugaba Donald Trump na Amurka yace zai taimaka wajen kawo karshen yakin da ake yi a kasar Sudan, a bayan da Yarima mai jiran gado na Sa’udiyya, Muhammad bin Salman, ya roke shi da ya sa baki a lamarin.

Shugaba Trump ya fada wajen wani taron zuba jari a Sa’udiyya jiya Laraba, cewa minti 30 a bayan da yariman na Sa’udiyya ya roke shi a lokacin ganawarsu ta ran Talata, gwamnatinsa ta fara daukar matakan ganin an kawo karshen yakin na Sudan.

Daga bisani shugaba Trump ya fada a wani rubutun da yayi a kafar sada zumunci cewa Amurka zata yi aiki tare da Sa’udiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa, da Masar da wasu kasashen na yankin Gabas ta Tsakiya domin kawo karshen zub da jini da daidaita al’amura a kasar Sudan.

Yarima bin Salman yayi amanna da cewa ana bukatar sa bakin shugaba Trump kai tsaye domin karya lagon cijewar da aka samu a tattaunawar kawo karshen wannan yaki da aka shafe shekaru biyu da rabi ana yi.

Warware wannan rikici na Sudan yana da matukar muhimmanci ga tsaron kasar Sa’udiyya a saboda iyaka mai tsawon daruruwan kilomitoci da tekun Bahar Maliya ta bi ta raba a tsakaninta da Sudan.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Wasu Zakaru Da Suka Samu Karramawar Hukumar CAF Ta Afrika
Next Post: Rasha Na Cigaba Da Kai Hare-Haren Makamai Masu Linzami Ga Ukrain

Karin Labarai Masu Alaka

Tattalin Arzikin Kasar Bahrain Ya Bunkasa Sakamakon Ruruwar Masu Yawon Bude Ido Labarai
Guterres: Babban Kuskure Ne Yadda Isra’ila Ta Kai Farmaki A Gaza Labarai
Kocin Zambia Na Mata Ba Lafiya Labarai
An Kafa Majalisar Kotun Sulhu Ta Kano Labarai
Margayi Shugaba Muhammadu Buhari 1942-2025 Labarai
Hukumar Zabe A Najeriya Ta Cigaba Da Rijistar Katin Zabe Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi
  • Kabiru Vice: Najeriya Zata Iya Nasara A Kan Moroko AFCON 2025.
  • Motar Yashi Ta Kashe Mutane Shida A Wani Coci Dake Legas
  • An Kaddamar Da Rijistar Zamani Ta Zamowa Mamba A Jam’iyar APC

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ronaldo Da Messi Ka Iya Hadu A Gasar Cin Kofin Duniya: Ta Ya Ya ? Wasanni
  • Abba Kabir: Zamu Samar da Jirage Marasa Matuka A Kano Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Shugaba Tinubu Ya Umurci Janyewa Manyan Mutane ‘Yan Sanda Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Dangote Ya Bukaci ICPC Ta Binciki Shugaban NMDPRA Najeriya
  • Jagoran Kasar Iran Yace Basa Bukatar Tallafin Kasar Amurka Afrika
  • Yanayin Sanyi Yayi Kamari a Yankin Gaza Tsaro
  • Jirgin Sama Mai Saukar Ungulu Ya Kashe Mutane Biyar A Tanzaniya Afrika
  • An Murkushe Wani Yunkurin Juyin Mulki A Jamhuriyar Benin Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.