Trump ya ce Amurka ta kai “hare-hare masu yawa” masu kisa kan ‘yan ta’adda a Najeriya.
Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump, ya ce a ranar Alhamis sojojin Amurka sun kai munanan hare-hare kan ‘yan ta’addar Daular Musulunci (ISIS) a Arewa maso Yammacin Najeriya, tare da yin barazanar ci gaba da kai hare-hare idan ‘yan ta’addan suka ci gaba da kashe kiristoci.

Shugaban ya bayyana hakan ne a shafinsa na X inda ya ƙara da cewa Ma’aikatar Yaƙi ta Amurka ta aiwatar da hare-hare masu nasara da dama.
Ya rubuta cewa, “Yau da daddare, bisa umarni na a matsayi na na Babban Kwamandan Sojojin Amurka ta kaddamar da wani mummunan hari mai ƙarfi kan ‘yan ta’addar ISIS a Arewa maso Yammacin Najeriya, waɗanda suka dade suna kai hari tare da kashe Kiristoci marasa laifi.
“A baya na yi gargaɗi ga waɗannan ‘yan ta’adda cewa idan ba su daina kisan Kiristoci ba, za su fuskanci mummunan sakamako, kuma a daren yau hakan ta faru.
“Ma’aikatar Yaƙi ta aiwatar da hare-hare masu tsari da nagarta da dama, irin waɗanda Amurka kaɗai ke iya aiwatarwa.
“A ƙarƙashin jagoranci na, ƙasar mu ba za ta bari ta’addancin Musulunci mai tsatsauran ra’ayi ya bunƙasa ba.
“Allah Ya albarkaci sojojin mu, kuma Barka da kirsimeti ga kowa, har da ‘yan ta’addar da aka kashe, waɗanda za su ƙaru idan suka ci gaba da kisan Kiristoci.”


