Daruruwan Tsoffin ma’aikatan Gwamnatin Jihar Nejan Najeriya ne Suka Gudanar da zanga zanga Domin nuna rashin jin dadin kin biyansu hakkokin su na barin aiki har na tsawon shekaru,
‘Yan fashon dai wadanda suka mamaye Babban dakin taro na Legbo kutigi dake daura da gidan Gwamnatin Jihar Nejan sunce wasu daga cikinsu sun share kimanin shekaru 7 zuwa 8 ba tare da an basu harkokinsu na barin aiki ba wato graduty,
Mr. Stevin Daniel Rita shine Shugaban tawagar tsoffin ma’aikatan da ake kira pressure group yace tura ce ta Kai bango shi yasa suka fito wannan zanga zanga…
To daga bisani dai Mataimakin Gwamnan Jihar Nejan Kwamred Yakubu Garba ya gana da ‘Yan fashon tare da daukar wani Sabon Alkawali na biyansu hakkokinsu sai dai ga Alama wasu daga cikin yan fanshon basu gamsu da alkawalin mataimakin Gwamnan ba.
Ma’aikatar Kula da harkokin fansho ta Jihar Neja dai tace tsoffin ma’aikatan su kara hakuri domin nan gaba kadan zasuyi dariya kamar yadda Malam Habibu Abdulkadir Babban Sakatare na ma,aikatar Fansho a Jihar Neja yayi Karin bayani..
A Najeriya dai ba Wani sabon abu bane aga tsoffin ma,aikata da suka sadaukar da rayuwarsu wajan yima kasarsu hidima Amma kuma sauran lokacin rayuwarsu ta kare da takaicin Rashin samun hakkokinsu na yin ritaya daga aiki.
Wakilin GTA Hausa Amurka Ke Magana a jihar Neja Mustapha Nasiru Batsari Yana dauke da cikekken rahoton


