Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maikaba Ya Yi Murabus A Matsayinsa Kocin Wikki Tourist FC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • NEDC : Zata Samar Da Cikekken Kulawa Wa ‘Yan Jaridar Da Sukayi Hatsari A Bauchi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Trump Zata Kafa Kasuwar Ma’adanai Amurka
  • An Yanke Mishi Hukuncin Kisa Saboda Neman Kudin Aure Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Babban Malamin Musulunci Sheikh Usman Kusfa Zaria Ya Rasu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Wakilan Majalisar Dokokin Phillipines Suna Yunkurin Tsige Shugaban Kasar
Published: February 3, 2026 at 10:16 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Ranar talata, wakilan majalisar dokokin Phillipines suka yi zama domin yanke shawarar ko su ci gaba da sauraron karar neman tsige shugaban kasar Ferdinad Marcos Jr., wanda ake zargi da cin amanar kasa, rashawa, da kuma keta tsarin mulkin kasar.

Shugaba Marcos wanda yake tsakiyar wa’adin mulkinsa na shekaru shida, wanda ya musanta zargin, yana Fuskantar tuhuma da wani lauya dan gwagarmaya ya shigar gaban majalisar.

Idan har majalisa ta amince da zargin da ake yi wa shugaba Marcos, zai kasance shugaban kasar Phillipines na biyu da za’a tsige, na farko shine shugaba Joseph Estrada, wanda shari’arsa a shekara ta 2001 ta wargaje lokacin da wasu masu gabatar da kara suka fice daga inda ake shari’ar.

Laifuffukan da lauyan yake zargin shugaban na Phillipines sun hada da laifin sa a kama tsohon shugaban kasar Rodrigo Dutarte da mika shi ga kotun kasa da kasa mai hukunta manyan laifuffuka kan zargin da kotun take yi wa Dutarte na kashe duban mutane lokacin mulkinsa karkashin shirin yaki da miyagun kwayoyi.

Haka nan Marcos yana Fuskantar zarginsa kan yadda aka kashe dukiyar al’umma da ya kai ga abun fallasa kan ayyukan kare jama’a daga bala’in ambaliyar ruwa, da kuma zargin da ake yiwa shugaban kasar na mafani da miyagun kwayoyi, wadda idan ya tabbata ba zai cancanci ci gaba da shugabancin kasar ba.

Afrika, Labarai

Post navigation

Previous Post: Kotun Uganda Tayi Watsi Da Karar Hukumomin Kasar
Next Post: Kotun Daukaka Kara A Faransa Zata Tabbatar Da Hukuncin ‘Yan Jam’iyyar Ra’ayin Rikau

Karin Labarai Masu Alaka

Gidauniya: An Fara Tiyatar ‘Hernia’ Da ‘Hydrocele’ Kyauta A Jihar Katsina Labarai
Trump Yayi Barazanar Goyon Bayan Hari Akan Kasar Iran Labarai
Wani Harin ‘Yan Bindiga Ya Kashe Mutane 35 A Jihar Borno Labarai
Karo Na Biyu Cikin Kwanaki 29 An Samu Gobara A Kasuwar Katako Labarai
Kasar Iceland Ta Kauracewa Bikin Gasar Wakokin Shekara Mai Zuwa Labarai
Kakakin Majalisar Kasar Amurka Yana Tsaka Mai Wuya Game Da Kasafin Kudi Amurka

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Indonesia Zata Kafafa Rundunar Kiyaye Zaman Lafiya A Gaza
  • Shugabannin Kasar Australia Sun Bukaci ‘Yan Kasar Suyi Zanga Zanga Cikin Lumana
  • Shugaban Afrika Ta Kudu Yanuna Goyon Bayan Kawo Karshen Yaki Tsakanin Rasha Da Ukraine
  • Ethiopia Tana Horas Da Dakarun RSF A Wani Sansani
  • Majalisar Dottijan Najeriya Ta Amince Da Tura Sakamakon Zabe Ta Na’ura

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Kasar Canada Ta Amince A Shigar Da Motoci Kirar Kasar China Kasar Amurka
  • Tattalin Arzikin Kasar Uganda Zai Bunkasa A Wannan Shekarar Labarai
  • Kocin Zambia Na Mata Ba Lafiya Labarai
  • Ministan Tsaro Ya Umarci Janye Sojoji Daga Shingayen Bincike A Tituna Najeriya
  • Kasar China Ta Sauka Daga Ragamar Bada Bashi Labarai
  • Boko Haram Sun Dauke Kansiloli A Borno Tsaro
  • Amurka Ta Yi Juyin Mulki A Kasar Venezuela Amurka
  • Gwamnatin Kebbi Ta Samu Tankokin Yaki Tsaro
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.