Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Amurka Ta Baiwa Najeriya Wasu Muhimman Kayan Yaki Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Trump Yayi Kira Ga ‘Yan Ƙasar Iran Su Ci Gaba Da Zanga Zanga Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Syria: Mutane Sun Yi Zanga Zanga Domin Nuna Rashin Amincewa Da Korar Kurdawa A Birnin Aleppo Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Wani Dan Bindiga Ya Harbi Dakarun Tsaron Cikin Gida Su Biyu A Washington DC
Published: November 27, 2025 at 7:14 PM | By: Nafisa Ahmad

Wani dan bindiga ya bude wuta ya harbi wasu dakarun tsaron cikin gida su biyu daga Jihar West Virginia da aka girka a nan Washington DC, dab da fadar White House, a wani lamarin da magajiyar garin birnin Washington ta bayyana a zaman hari na gangan a kan sojojin.

Darektan hukumnar binciken manyan laifuffuka ta tarayya, Kash Patel, da magajiyar garin birnin Washington, Muriel Bowser, sun ce dakarun suna kwance a asibiti, rai a hannun Allah.

Irin wannan farmaki na ba-saban ba a kan dakarun tsaron cikin gida yana zuwa a daidai lokacin da ake ta ci gaba cacar baki kan girka irin wadannan dakaru a nan Washington da wasu birane, inda aka yi wata da watanni ana shigar da kararraki a kotuna da yin zaga-zanga kan yadda gwamnatin Trump take amfani da sojoji don takalar abinda ta kira matsalar aikata laifuffuka.

Shi ma wanda ake zargin cewa dan bindigar ne, an harbe shi kuma na kama shi, amma ana jin rauninsa ba mai tsanani ba ne.

Nan da nan gwamnatin Mr. Trump ta bada umurnin da a kara turo karin dakarun tsaron cikin gida dari biyar (500) zuwa nan Washington.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Gobara Mafi Muni Cikin Shekaru 60 A Hong Kong Ta Hallaka Rayuka
Next Post: ECOWAS Da AU Sun Nuna Damuwa Kan Juyin Mulki A Guinea-Bissau

Karin Labarai Masu Alaka

Mala Buni: Zai Jagoranci Kwamitin Sassanci Na Jam’iyar APC Labarai
Shugaba Trump Yace Amurka Ce Zata Rika Gudanar Da Harkokin Kasar Venezuela Amurka
Majalisar Tarayya Ta Amince Da Gyara Dokar Kasafin Kudi Labarai
Yakin Rasha Da Ukrain Babban Kalubale Ne Ga Kasashen Turai Labarai
Gwamnan Jihar Filato Ya Karbi Katin APC Labarai
Anfara Samun Sakamakon Wucin Gadi a Kasar Guinea Conakry Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Najeriya Ta Dauki Hayan Amurkawa Don Kyautata Alaka Da Trump Game Da Kisan Kiristoci
  • Gwamnatin Tarayya Ta Cimma Yarjejeniya Da Kungiyar Malaman Jami’oi
  • Kabiru Vice: Najeriya Zata Iya Nasara A Kan Moroko AFCON 2025.
  • Motar Yashi Ta Kashe Mutane Shida A Wani Coci Dake Legas
  • An Kaddamar Da Rijistar Zamani Ta Zamowa Mamba A Jam’iyar APC

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ministan Kudin Najeriya: Bamu Samu Kudaden Da Muke Tsammani A Wannan Shekarar Ba Najeriya
  • Gwamna Abba Gida-Gida Na Dari-Darin Shiga APC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Hari Akan Wata Mashaya Ya Rutsa Da Mutane 9 A Afirka Ta Kudu Afrika
  • Sojojin Amurka Sun Kashe Wasu Fararen Hula Ba Dalili Amurka
  • Tsohon Alkalin Alkalai A Najeriya Ya Rasu Yana Da Shekaru 71 Labarai
  • Jirgin Sama Mai Saukar Ungulu Ya Kashe Mutane Biyar A Tanzaniya Afrika
  • Wikki Tourist FC: Ta Sallami ‘Yan Wasa Hudu Wasanni
  • Gwamnatin Gombe Ta Raba Naira Miliyan 14 Ga Iyalen ‘Yan Jaridan Da Suka Rasu Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.