Kungiyar kiristocin Najeriya wato CAN reshen Jihar Neja ta sanar da cewa yara 50 daga cikin wadanda ‘yan bindiga suka sace a ranar Juma’ar da ta gabata a Makarantar St. Mary ta Papiri sun samu nasarar kubutowa daga hannun ‘yan bindigar.
Dama dai tun aranar Lahadi kungiyar tace sama da yara 300 ne ‘yan bindigar su kayi awon gaba dasu a wannan Makaranta waddake mallakar Cocin Katolic ce.

Mai magana da yawun kungiyar ta CAN a Jihar Mr. Dan Atory ya tabbatar da cewa yara 50 sun gudo daga hannun ‘yan bindigar kuma yanzu haka suna tare da iyayensu.
”Yace Jiya Lahadi mun samu kyakkyawan Labari Domin yaran sun samu wani wuri sun boye daga baya suka gudu daga dajin suka boye wani wuri, to ya zuwa Jiya Lahadi yara 50 sun koma hannun iyayensu”

To Sai dai har ya zuwa wannan rana ta Litanin Hukumomin Jihar Nejan basu da masaniya akan yaran da kungiyar ta CAN tace sun kubuto daga hannun ‘yan bindigar.

Kwamishinan yan sanda na Jihar Neja CP Adamu Elleman yace har yanzu hukumomin wannan Makaranta ta St. Mary basu bada bayanin komi ba kamar yadda yayi karin bayani a zantawarmu ta wayar Salula.


