Ƴan Agajin Izala Sun Tsallake Rijiya da Baya a Hatsarin Mota a Hanyarsu Daga Bauchi
Ƴan agajin ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Iqamatis Sunnah (Izala) reshen Jihar Gombe sun tsallake rijiya da baya, bayan da motarsu ta yi hatsari a hanyar su ta dawowa daga jihar Bauchi, inda suka halarci Kamfin na ƴan agaji.

Rahotanni sun tabbatar da cewa babu asarar rai a hatsarin, sai dai wasu daga cikin su sun samu raunuka daban-daban kuma an garzaya da su zuwa asibiti domin samun kulawar gaggawa daga likitoci.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa jami’ai da masu agajin gaggawa sun kai ɗauki cikin hanzari, wanda ya taimaka matuƙa wajen rage illar da hatsarin zai iya haifarwa.
Shugabannin ƙungiyar da al’ummar yankin sun nuna godiyar su ga Allah Madaukakin Sarki bisa kare rayukan ƴan agajin, tare da yin addu’ar samun sauƙi cikin gaggawa ga waɗanda suka samu raunuka.


