A halinda ake ciki kuma a Uganda, yansandan kasar sun bada sanarwar cewa sun tsare wata ‘yar fafutuka mai rajin kare hakkin Bil’adama Sarah Bireete, a lokacinda gwamnatin shugaba Yuweri Museveni wacce ta juma tana mulkin kasar, ta na fada da matakan murkushe ‘yan adawa da masu sukar lamirinta, gabannin zaben kasar da za yi ranar 15 ga watan gobe.
Bireete, wacce take jagoranci ga wata kungiyar kare hakkin Bil’adama, kuma maiyawan fita a gidajen radio da talabijin tana sharhi da sukar gwamnatin, ‘yansandan kasar sun tabbatar labarin tsare ta a wani sako data wallafa jiya talata shafinta a dandain X.
“Tana hanun ‘yansanda, za’a gurfanar da ita agaban kotu nan bada jumawa ba.
Kamar yaddaa bayanai da rundunar ta bayar, sai dai sanarwar bata bada ranar da za’a gurfanar da ita ko laifin da ake tuhumarta akai ba.
Malama Bireete wacce lauya ce, kuma shugabar kungiyar da ake yiwa lakabi da CCG watau center for constitutional government da turanci, tana sukar matakan gwamnati daban daban, ciki harda zargin tana tsare ‘yan hamayya ba bisa ka’ida ba, da kuma cin zarafin su.


