Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Dakarun Operation Fansan Yamma Sun Ceto Mutane 48 Da Aka Yi Garkuwa Da Su Afrika
  • NDLEA Ta Kama Dan Kasuwa Da Ke Yunkurin Safarar Hodar Iblis Afrika
  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama Afrika
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara Afrika
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe Afrika

Yobe Ta Sake Jaddada Ƙudirin Rage Mutuwar Yara
Published: July 7, 2026 at 6:44 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin jihar Yobe dake arewa maso Gabashin Najeriya ta sake jaddada aniyarta na rage yawan mutuwar yara masu ƙasa da shekara biyar ta hanyar ci gaba da aiwatar da shirin SARMAAN, tare da shirye-shiryen faɗaɗa shi zuwa dukkan ƙananan hukumomi 17 na jihar.

Ana gudanar da shirin ne na haɗin gwiwa da African Field Epidemiology Network (AFENET) Nigeria, inda aka faɗaɗa shi daga ƙananan hukumomi 10 a matakin farko zuwa 13 a zagayen da ake gudanarwa a halin yanzu.

Babban Jami’in Hulɗa da Gwamna kan Kula da Lafiya a Matakin Farko, Dakta Umar Ciroma, ya ce shirin ya samo asali ne daga shawarar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ga ƙasashen da ke fama da yawan mutuwar yara masu ƙasa da shekara biyar.

Ya bayyana cewa ana bai wa yara ƙwayar maganin Azithromycin sau shida cikin tsawon shekaru uku, ana ba su duk bayan watanni shida, domin kariya daga wasu cututtukan ƙwayoyin bacteria da ke haddasa ciwon huhu, cutar sepsis, cututtukan fata, trachoma da kuma wasu nau’ikan gudawa.

Al’ummomi da dama a faɗin jihar sun ci gaba da karɓar shirin hannu bibbiyu, inda iyaye da masu kula da yara suka bayyana cewa sun lura da ingantuwar lafiyar yaransu bayan karɓar maganin.

Haka kuma, Cibiyar Binciken Lafiya ta Najeriya (NIMR) na sa ido tare da tantance tasirin shirin wajen tabbatar da cewa duk wani mataki na gaba zai kasance bisa hujjojin kimiyya.

Masu ruwa da tsaki sun ce haɗin gwiwar gwamnati, ma’aikatan lafiya, abokan hulɗar ci gaba da al’ummomi na ƙara wa jama’a kwarin gwiwa kan shirin, tare da ƙarfafa ƙoƙarin rage mutuwar yara da za a iya kauce wa a jihar Yobe.

Afrika, Kimiya, Kiwon Lafiya, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Rundunar ‘Yan Sandan Kebbi Ta Dakile Yunkurin Garkuwa Da Mutune, Ta Kama Masu Laifi
Next Post: ‘Yan Sandan Bauchi Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Fashi da Makami A Gadau

Karin Labarai Masu Alaka

Jam’iyar SDP Tana Gudanar Da Babban Taro A Bauchi Afrika
Kama Muhyi Magaji Siyasa ce Kawai Inji Gwamnatin Kano Labarai
Rangadin Ayyukan Tinubu Ya Kai Tawaga Zuwa Kano Northern Bypass Afrika
Gwamnonin Arewa Sunyi Allah Wadai Da Harin Jos Afrika
Kasashen Yankin Gulf Sun Bada Sanarwa Afrika
An Kai Hari Babbar Tashar Iskar Gas A Iran Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Dakarun Operation Fansan Yamma Sun Ceto Mutane 48 Da Aka Yi Garkuwa Da Su
  • NDLEA Ta Kama Dan Kasuwa Da Ke Yunkurin Safarar Hodar Iblis
  • Sojojin Najeriya Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama
  • An Sace Wani Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Zamfara
  • Aikin Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Ya Samu Gagarumar Nasara A Gombe

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Alkalan Wasannin Kwallon Kafa A Ghana Zasu Samu Inshora Wasanni
  • Shirin Dare 2030 UTC Yau Asabar 11.22.2025 Rediyo
  • Ƙungiyoyin Premier 17 Za Su Rasa ‘Yan Wasa 40 saboda Gasar AFCON 2025, Wasanni
  • Amurka Zata Kamallah Yaki Da Iran A Makonni Biyu Masu Zuwa Amurka
  • Sabon Ma’aikacin Tsaro Ne Ya Kashe Amurkawa Amurka
  • Sojojin Najeriya Sun Kashe Fitaccen ’Yan Bindiga Kallamu A Jihar Sakkwato Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • An Tsinto Gawarwakin ‘Yan gudun Hijira A Bakin Tekun Comoros Labarai
  • Kimanin Ganga Miliyan 40 Na Danyen Albarkatun Mai Yayi Kwantai A Kasashen Afirka Ta Yamma Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.