Hare-haren makamai masu linzami da jiragen drone da Rasha ta kai yau talata sun kashe mutane akalla uku cikinsu har da karamin yaro daya a Ukraine, tare da haddasa daukewar wutar lantarki a sassa da dama.
Wadannan hare-haren dake zuwa a bayan wani sabon zagaye na tattaunawar neman kawo karshen yakin na shekaru 4, sun fi lahani ga cibiyoyin samar da wutar lantarki na yammacin kasar.
Kasar Poland wadda ke makwabtaka da Ukraine a yamma, sai da ta tayar da jiragen saman yakinta a saboda hare-haren sun wakana dab da bakin iyakarta.
Shugaba Volodymyr Zelensky yace Rasha ta kai hare hare a kan yankuna akalla 13 na kasar.
Rasha ta ce ta kai hari a kan cibiyoyin samar da makamashi da na soji na Ukraine, ta kuma kama wasu kananan garuruwa biyu a bakin daga, amma ba a ji ta bakin kasar Ukraine kan wannan ba, kuma an san a baya tana musanta duk wani ikirarin Rasha na samun galaba a bakin daga.
Ita ma Ukraine ta kai nata harin cikin daren a kan wata masana’anta a yankin Stavropol na kudancin Rasha, ta haddasa tashin wuta a wurin a cewar gwamnan wannan yanki, Vladimir Vladimirov.


