Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • PDP Ta Tsayar da Goodluck Jonathan Takarar Shugaban Kasa Afrika
  • Hawan Gidan Gwamnati A Jihar Gombe Afrika
  • Hawan Babbar Sallah A Masarautar Kaltungo Dake Jihar Gombe Afrika
  • Sarkin Gombe Ya Yabi Nasarorin Inuwa Yahaya A Fannonin Tsaro Da Raya Kasa Afrika
  • Tinubu Ya Jaddada Aniyar Rage Tsadar Rayuwa Da Samar da Ayyukan Yi Afrika

Tinubu: Mun Ware Biliyan 42 Don Inganta Lafiyar ‘Yan-Kasa
Published: January 11, 2026 at 3:26 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: January 11, 2026

Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan 42 don kula da lafiyar ‘yan Najeriya miliyan 10 masu ƙaramin ƙarfi a 2026.

Gwamnatin Tarayya ta gabatar da kudirin ware Naira biliyan 42.18 domin samar da muhimman ayyukan kiwon lafiya ga ‘yan Najeriya miliyan 10 da ake ganin suna cikin masu rauni, a cikin kasafin kudin shekarar 2026 da aka gabatar wa Majalisar Tarayya.

Wannan kudin na daga cikin jimillar Naira tiriliyan 2.48 da aka ware wa bangaren kiwon lafiya a kasafin kudin shekarar, inda aka tanadi kudaden domin sayen magunguna, kayan amfani a asibitoci, kayayyakin aikin likitanci, sinadaran gwaje-gwaje da kayan gwajin cututtuka, da nufin inganta samun kulawar lafiya musamman ga talakawa a fadin kasar.

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya mika kudirin kasafin kudin shekarar 2026 ga majalisar Dokoki ta Kasa a watan da ya gabata, inda ya bayyana muhimman abubuwan da gwamnatinsa ta bawa fifiko a daidai lokacin da kasar ke fuskantar kalubalen tattalin arziki da zamantakewa.

A cewar bayanan kasafin kudin, bangaren tsaro da kariya ne ya samu kaso mafi tsoka da Naira tiriliyan 5.4, sai bangaren gine-ginen ababen more rayuwa da Naira tiriliyan 3.56, ilimi da Naira tiriliyan 3.52, sannan kiwon lafiya da Naira tiriliyan 2.48, wanda ya zama bangare na hudu mafi girma a jerin fifikon kashe kudin gwamnati.

Daga cikin jimillar kasafin kudin Tarayya na Naira tiriliyan 58.47, kudin da aka ware wa kiwon lafiya ya kai kusan kashi 4.2 cikin 100. Wannan kasafin ya kunshi shirye-shirye daban-daban na rigakafin cututtuka, samar da ayyukan lafiya, sayen kayan aikin asibiti, da tallafa wa rukunin al’umma masu rauni.

A jawabinsa yayin gabatar da kasafin kudin, Shugaba Tinubu ya jaddada muhimmancin bangarorin kiwon lafiya da ilimi wajen gina jari na bil’adama, yana mai cewa babu wata kasa da za ta ci gaba fiye da ingancin mutanenta.

Shugaban kasar ya kuma bayyana rawar da abokan hulda na kasa da kasa ke takawa wajen tallafa wa tsarin kiwon lafiyar Najeriya, inda ya ce tattaunawa da gwamnatin Amurka ta samar da damar samun tallafin fiye da dala miliyan 500 domin aiwatar da muhimman shirye-shiryen lafiya a kasar.

Labarai

Post navigation

Previous Post: Habasha Tafara Gina Filin Jirgin Sama Mafi Girma A Afirka
Next Post: CAF Ta Fara Binciken Rikicin Bayan Wasa Tsakanin Algeria Da Najeriya

Karin Labarai Masu Alaka

Jarman Deba Ya Kada Senata Goje A Zaben Fidda Gwani Afrika
Wasan Hamayya (Istanbul Derby) Fenerbahçe Da Galatasaray 1-1 Labarai
Shugaba Tinubu Ya Turawa Majalisa Sunayen Mutane Biyun Da Zasu Shugabanci Sashin Albarkatun Mai Labarai
Wani Jirgin Sama Ya Karya Dokar Hana Zirga Zirga Amurka
Tinubu Ya Jaddada Aniyar Rage Tsadar Rayuwa Da Samar da Ayyukan Yi Afrika
Harin Da Israela Ta Kai Gaza Yayi Ajalin Mutane 27 Da Yara Uku Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • PDP Ta Tsayar da Goodluck Jonathan Takarar Shugaban Kasa
  • Hawan Gidan Gwamnati A Jihar Gombe
  • Hawan Babbar Sallah A Masarautar Kaltungo Dake Jihar Gombe
  • Sarkin Gombe Ya Yabi Nasarorin Inuwa Yahaya A Fannonin Tsaro Da Raya Kasa
  • Tinubu Ya Jaddada Aniyar Rage Tsadar Rayuwa Da Samar da Ayyukan Yi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Gwamnatin Najeriya Taja Hankalin ‘Yan Najeriya Mazauna Iran Da Kasashen Larabawa Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Tsofin Shugabanin Kasa Sun Karbi Bakoncin Hafsan Sojin Najeriya Tsaro
  • Onana Ba Ya Cikin Tawagar Kamaru (AFCON) Wasanni
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Fiye Da Mutane 50 Tare Da Sace Mata Da Yara A Jihar Zamfara Najeriya
  • Amurka Zata Tantance Fararen Fata ‘Yan Afirka Ta Kudu Afrika
  • Kungiyoyin Mata A Jihar Filato Sunyi Gangamin Samun Jagorancin Siyasa Afrika
  • Wasu Mutane 15 Sun Rasa Rayukan Su A Gabashin Kwango Afrika
  • Jami’an Tsaron Pakistan Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.