Kamfanin safarar jiragen saman Ethiopian Airlines ya fara gagarumin aikin ginin wani sabon filin sauka da tashin jiragen saman da za a kashe zunzurutun kudi har dala biliyan 12 da rabi wajen kera shi, wanda kuma jami’ai suka ce zai zamo filin jirgin sama mafi girma a nahiyar Afirka idan aka kammala shi a shekarar 2030.
An bawa kamfanin safarar jiragen saman aikin tsarawa da kuma aiwatar da wannan fili mai hanyoyi 4 na sauka da tashin jirage a garin Bishoftu, mai tazarar kilomita 45 daga Addis Ababa, babban birnin kasar.
Firayim minista Abiy Ahmed Ali ya fada a shafinsa na dandalin X cewa, aikin gina filin jirgin saman kasa da kasa na Bishoftu, kuma zai zamo aiki mafi girma da ya shafi zirga-zirgar jiragen saman a tarihin nahiyar Afirka kuma Filin jirgin zai zamo yana da wurin ajiye jiragen sama guda 270 a lokaci guda, kuma zai iya karbar fasinja miliyan 110 a duk shekara.
Wannan adadi zai ninka yawan fasinja dake iya amfani da filin jirgin saman Bole da ake amfani da shi a yanzu har sau 4, Firayim minista Abiy yace nan da shekara biyu zuwa uku, filin jirgin saman na Bole zai kure yawan fasinja da jirage da zai iya karba.
Kamfanin safarar jiragen saman Ethiopian Airlines zai samar da kashi 30 cikin 100 na kudin aikin, yayin da masu bayar da rance zasu samar da sauran kuma Tuni har kamfanin ya ware dala miliyan 610 don fara aikin tono da gyaran inda za a yi filin jirgin.


