Allah ya yiwa fitaccen ɗan jarida Surajo Dalhatu Sifawa Sokoto rasuwa a cikin daren wannan yini na Laraba.
A cikin wata sanarwar da shugaban kungiyar yan jarida ta Najeriya (NUJ) reshen jihar Sokoto Usman Binji ya fitar a yau, an bayyana alhinin ilahirin ƴaƴan ƙungiyar kuma ta mika saƙon ta’aziyyarta ga iyalai da ƴan uwa da abokan marigayin.
Kafin rasuwarsa, marigayi Surajo Sifawa shi ne Santurakin Sifawa, kuma ma’aikaci ne a hukumar kafafen watsa labarai ta jihar Sokoto, wato Sokoto State Media Corporation.
Ya rasu kwanaki kaɗan bayan rasuwar mahaifinsa.
Za a yi masa sutura a gidansa da ke Unguwar Arkilla (hanyar zuwa BIGA College) a birnin Sokoto, da misalin ƙarfe 11 na safiyar laraba.


