Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Kasar Togo Ta Kori Paul Henri Damiba Zuwa Kasar Sa Ta Haihuwa
Published: January 21, 2026 at 5:38 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Hukumomi a kasar Togo sun kame tare da korar tsohon shugaban kasar Burkina Faso, Paul Henri Damiba, zuwa kasar sa ta haihuwa, bayan da gwamnati ta zarge shi da laifin yunkurin juyin mulki, kamar yadda wasu majiyoyi 2 suka shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters ranar Talata.

Paul Henri Damiba, ya karbi ragamar mulki ne a shekarar 2022, bayan da aka yiwa gwamnatin farar hula ta Burkina faso juyin mulki, wadda farin jinin ta ya dusashe saboda yawan tashin hankali da ake samu daga ‘yan ta’adda.

Rashin nasarar Damiba wajen dakile hare-haren ‘yan ta’adda, ya haifar da fushin sojin kasar, abinda ya jawo shima aka tsige shi a wannan shekarar, a wani juyin mulki karkashin Ibrahim Traore, wanda a yanzu shi ne shugaban kasar karkashin mulkin soja.

A farkon Wannan watan ne Burkina Faso ta sanar cewa ta dakile wani yunkuri na kashe shugaba Traore, da ake zargin Damiba ne ya shirya, wanda ya nemi mafaka a Lome, babban birnin kasar Togo.

Wani jami’in tsaro da wani dake da kusanci da shugaban kasar Togo sun shaidawa kamfanin dillacin labarai na Reuters ranar Talata cewa An kama Damiba ranar Asabar, kuma An dauke shi a jirgi zuwa Ouagadougou, babban birnin Burkina Faso.

Togo ta tabbatar da fitar da Damiba daga kasar, inda ta ce ta yi haka ne, bisa bukata daga Burkina Faso.

Laifukan da ake tuhumar Damiba a Burkina Faso da su sun hada da almubazzaranci da wadaka da kudaden al’umma da halarta kudin haram, a cewar gwamnatin Togo

Afrika, Labarai

Post navigation

Previous Post: Sojin Najeriya Da ‘Yan Ta’adda Sunyi Taho Mugama
Next Post: Turkiyya Tana Gudanar Da Binciken Kasar Da Suka Kona Tutar Ta

Karin Labarai Masu Alaka

“Yan Wasan Super Eagles Sun Karbi Alkawarin Da Gwamnati Tayi Musu AFCON 2023 Labarai
Tsananta Hukunci Ga Masu Fyade Kan Takaita Cin Zarafin Yara Labarai
‘Yan Jaridar Gidan Gwamnatin Bauchi Sun Kammala Taron Horo Kan Fasahar Sadarwar Zamani Afrika
Isra’ila Ta Cire Sunayen Wasu Mutane Biyu Cikin Wadanda Take Fako Afrika
Mataimakin Shugaban Kasa Ya Sauka A Jihar Kwara Labarai
Akwai Yiwuwar Farashin Mai Zai Kara Tashi Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Ganduje Ya Nisanta Kansa Da Batan Dadiyata Labarai
  • Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Yi Gargaɗi Ga Masu Karya Dokokin Hanya Afrika
  • Wasan Hamayya (Istanbul Derby) Fenerbahçe Da Galatasaray 1-1 Labarai
  • Rashin Kyawun Hanyoyi Babbar Matsalace A Najeriya Afrika
  • Barayin Waya Sun Yanke Yatsun Hannu Guda Biyu Da Gefen Kunne A Bauchi Labarai
  • Dubban Mutane Sunyi Zanga-Zanga A Kasar Australia Afrika
  • Masoya Kungiyar Kwallon Kafar Morocco Suna Cikin Farin Ciki Bisa Hukuncin Kotu Afrika
  • Gwamnatin Trump Zata Kafa Kasuwar Ma’adanai Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.