Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

INEC: Akwai Yiwuwar Dage Zaben 2027 Saboda Azumi
Published: February 14, 2026 at 4:03 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta ce tana ci gaba da tuntuba kan jadawalin babban zaɓen 2027, bayan da aka nuna damuwa cewa ranar zaɓen ta yi daidai da watan Ramadan.

A wata sanarwa da Kwamishinan Ƙasa kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Masu Zaɓe, Mohammed Haruna, ya fitar, hukumar ta ce an tsara ranakun ne bisa tanadin Kundin Tsarin Mulki na 1999 da dokar zaɓe ta 2022 da kuma ƙa’idojin INEC.

INEC ta sanya 20 ga Fabrairu, 2027 domin zaɓen Shugaban Ƙasa da na Majalisar Dokoki ta Ƙasa, yayin da zaɓen gwamnoni da na majalisun dokokin jihohi zai gudana a 6 ga Maris, 2027.

Sai dai wasu ‘yan Najeriya, ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, sun buƙaci a sake duba ranakun, suna mai cewa sun faɗa cikin watan azumi, wanda ka iya shafar yawan fitowar masu zaɓe.

Haruna ya ce hukumar na duba lamarin, kuma idan buƙatar hakan ta taso, za ta nemi matakin Majalisa domin tabbatar da gudanar da zaɓe mai haɗa kowa da kowa.

Labarai, Najeriya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Ganduje Ya Nisanta Kansa Da Batan Dadiyata
Next Post: Usman Maiyama Ne Gwarzon Kamun Kifin Argungu Bana

Karin Labarai Masu Alaka

Iran Ta Tsagaita Kai Hare Hare Makwabta Afrika
Shugaban Mulkin Soja A Mali Ya Kirkiro Mukami Kamar Minista Afrika
Gwamnatin Najeriya Zata Farfado Da Cibiyar Koyon Sana’oi Ta Dangote Afrika
Gwamnatin Benue Da MACBAN Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Marigayi Ardo Risku Mohammed Afrika
An Gudanar Da Idin Karamar Sallah A Birnin Niamey Labarai
Hawan Nasarawa A Jihar Kano Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Jihar Kano Tayi Rashin ‘Yan Majalisu Biyu Najeriya
  • Birtaniya Zata Hana Jiragen Ruwan Rasha Wucewa Afrika
  • Iran Ta Harbo Jiragen Yakin Amurka Biyu Amurka
  • Gwamnonin Arewa Sun Kaddamar da Kwamitin Asusun Tsaro Afrika
  • Anyi Jana’izar Dan Majalisar Wakilai Yaya Bauchi Tongo Afrika
  • Matatar Man Dangote Zata Bada Kwangilar Sayar Da Gas Da Man Jirage Afrika
  • Majalisar Dattawa Ta Wanke Janar Christopher Musa A Matsayin Minista Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Kungiyar Maharba Da ‘Yan Sintiri Sun Samu Kyautar Motoci Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.