Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Za’a Ninka Shekarun Zama A Gidan Kurkuku Ga Masu Auren Jinsi A Senegal
Published: February 25, 2026 at 12:34 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Prime ministan kasar Senegal, Ousmane Sonko ya nemi a dabbaka dokar da zata ninka zama gidan kurkuku daga shekara 5 zuwa 10 ga duk wadanda aka kama da yin auren jinsi, da sauran abubuwa da suka jibanci irin wannan halayya.

Da yake jawabi ga majalisar kasar a ranar Talata, Sonko ya ce, dokar zata shafi duk wata dangantaka da bata dace ba tsakanin jinsin mutane daya, kuma duk wanda aka kama yana irin wannan alaka da wanda bai kai shekaru 21 ba, zai fuskanci cikakken hukunci.

Wadanda aka kama da laifi kuma zasu iya fuskantar tara daga sefa miliyan biyu zuwa miliyan 10 wanda yayi daidai da dala 3,590 zuwa dala 17,953.

Sonko yayi kira ga ‘yan majalisar kasa daga kowacce jam’iyya da su goyi bayan dokar, ya kuma zargi kasashen yamma da tallata goyon baya ga ‘yancin masu auren jinsi a Senegal, da kuma jawo rudanin siyasa.

Afrika, Labarai

Post navigation

Previous Post: Dakarun Sakai A Kasar Sudan Sun Kashe Mutane 28 A Wani Farmaki
Next Post: Harin Jirgi Marar Matuki Ya Kashe Kakakin ‘Yan Tawayen M23

Karin Labarai Masu Alaka

Kamfanin Dangote Zai Sayo Na’urori Daga Kasar China Kimiya
Ethiopia Tana Horas Da Dakarun RSF A Wani Sansani Afrika
An Bukaci Matasa Su Taka Gagarumar Rawa Wajen Gina Zaman Lafiya A Arewa Maso Gabas Afrika
Zulum Ya Tallafa Wa Mambobin NYSC Da Naira Miliyan 8.2 A Borno Afrika
‘Yan Bindiga A Mali Sun Kashe Direbobin Manyan Motoci Afrika
ECOWAS Da AU Sun Nuna Damuwa Kan Juyin Mulki A Guinea-Bissau Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Nijar: Zamu Tsananta Bincike A Bakin Iyakokin Mu Afrika
  • Jam’iyyar APC Ta Ayana Jamilu Gwamna A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Gombe Afrika
  • GOSEMA Ta Horar Da Mambobin LEMCs A Jihar Gombe Afrika
  • Gwamnatin Trump Zata Kafa Kasuwar Ma’adanai Amurka
  • Ministocin Kasar Asia Zasu Gudanar Da Taro A Kasar Malaysia Tsaro
  • An Saka Dokar Hana Fita A Karamar Hukumar Lamurde Jihar Adamawa Tsaro
  • Shugaba Tinubu Ya Gana Da Takwaransa Na Kasar Jamus Akan Sha’anin Tsaro Labarai
  • NEDC Ta Fara Shirin Kera Sanitary Pads A Gombe Domin Samar Da Sana’o’i Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.