Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Wata Biyu Najeriya Bata Bada Lasisin Shigo Da Mai Daga Ketare Ba
Published: March 11, 2026 at 8:24 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Wata biyu a jere, Najeriya bata bada lasisin shigo da man fetur daga ketare ba, yayinda hukumomin kasar suka fara aiki da dokar kasar data ce Najeriya zata bada izinin a shigo da mai daga ketare ne kawai idan ta fuskanci karanci a cikin gida.

Alkaluma daga hukumomin kula da harkokin mai na kasar sun nuna cewa ba’a bada lasisin shigo da mai cikin watan Febwairu ba, haka nan Kungiyar masu masana’antun tace mai suna cewa zuwa yanzu dai cikin watan Maris ba su ga an bada lasisin shigo da mai daga ketare ba. Idan hakan ya dore ya nuna nasara da kamfanin tace mai na Dangote ya samu, wadda a bara ya shigar da kara a gaban kotu na neman hana shigo da mai daga ketare.

A wani al’amari na daban, ranar Litinin ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ta gargadi ‘yan kasarta da suke Najeriya cewa akwai “barazanar harin ta’addanci,” kan muradun Amurka a kasar da suka hada da makarantu, kamar yadda sanarwar da ta bayar a ranar Litinin.

Ofishin jakadancin yana cikin Shirin ko ta kwana, tun lokacin da Amurka da Isra’ila suka kaddamar da hare hare kan Iran. Ofishin jakadancin ya bukaci Amurkawa da suyi taka-tsan tsan idan za su ziyarci ofishin jakadancin dake Abuja da kuma Legas, da kuma makarantu masu alaka da ita.

Labarai, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Shugaban Majalisar Tarayyar Turai Yace Rasha Tana Cin Ribar Yakin Gabas Ta Tsakiya
Next Post: ‘Yan Bindiga A Mali Sun Kashe Direbobin Manyan Motoci

Karin Labarai Masu Alaka

Kasar Ghana Ta Tono Gold Na Miliyoyin Kudade Kimiya
Jama’a A Yankin Gulf Sun Bukaci Dakatar Da Hare Hare Daga Washington Afrika
Rundunar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Shirya Taron Masu Ruwa Da Tsaki A Jihar Filato Afrika
Tattalin Arzikin Kasar Congo Ya Bunkasa Labarai
Jami’an Tsaro Sun Dakile Safarar Makamai Daga Jos Zuwa Jihar Neja Afrika
Magajin Garin Istanbul Dake Kurkuku Ya Bukaci A Gudanar Da Zabe Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaban Kasar Ukraine Yace Rasha Tana Bawa Iran Bayanan Sirri Afrika
  • ‘Yan Bindiga Suna Cigaba Da Cin Karensu Babu Babbaka A Najeriya Afrika
  • Dan Hamayya Ya Amince Da Faduwa A Zaben Kasar Benin Afrika
  • Gwamnatin Kasar Nijar Ta Kame Babban Dan Jarida Afrika
  • Addini Ko Kabilanci Basu Da Gurbi Cikin Ta’addanci Labarai
  • Tinubu, Akpabio da Ministoci 9 Zasu Tafi Ƙasar Birtaniya Afrika
  • An Canza Shugabannin Hukumar Hakar Ma’adanai A Congo Labarai
  • Gwamnatin Najeriya Ta Samar Da Wuta Mai Aiki Da Hasken Rana A Jami’ar ADUSTECH Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.