Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Kira Ga Haɗin Kai Domin Bunƙasa Maɗaba’u Afrika
  • Mataimakin Shugaban kasar Najeriya Ya Kaddamar Da Taron Zuba Jari A Jihar Jigawa Afrika
  • Uwargidan Shugaban Ƙasar Najeriya Ta Ƙaddamar Muhimman Ayyuka A Jihar Jigawa Afrika
  • Gwamnatin Najeriya Ta Fara Aikin Babbar Hanyar Da Za Ta Haɗa Jihohin Arewa Afrika
  • Gwamnatin Benue Da MACBAN Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Marigayi Ardo Risku Mohammed Afrika

Gwamnatin Najeriya Ta Ayyana Ranakun Hutun Sallar Azumi
Published: March 17, 2026 at 4:14 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana ranakun Alhamis 19 ga Maris da Juma’a 20 ga Maris, 2026 a matsayin ranakun hutun ƙasa domin bikin Ƙaramar Sallah (Eid-ul-Fitr).

Sanarwar ta fito ne ta bakin Babbar Sakatare a Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Magdalene Ajani, wadda ta ce Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayar da umarnin ayyana hutun a madadin Gwamnatin Tarayya.

Ministan ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan, inda ya buƙace su da su ci gaba da riƙe kyawawan ɗabi’u da suka koyu a lokacin azumin, ciki har da soyayya, karamci, haƙuri da sadaukarwa.

Haka kuma, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi amfani da wannan lokaci na bukukuwa wajen yi wa ƙasa addu’o’in zaman lafiya, haɗin kai da cigaba mai ɗorewa.

Tunji-Ojo ya kuma yi kira ga jama’a da su gudanar da shagulgulan Sallah cikin natsuwa tare da miƙa hannu ga marasa galihu, domin su ma su more farin cikin wannan lokaci na ibada.

Afrika, Labarai, Najeriya, Nishadi

Post navigation

Previous Post: Kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya Tayi Kakkausar Lafazi Game Da Harin Maiduguri
Next Post: An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko

Karin Labarai Masu Alaka

An Bukaci Sabbin Shugabanni Su Yi Jagoranci Nagari da Inganta Ayyukan Jama’a Labarai
NAHCON Ta Kaddamar da Tawagar Malamai Afrika
Kasuwannin Hannun Jari Sun Farfado Afrika
Shugabannin Kiristoci Sun Taya Musulmi Murnar Sallah Domin Ƙarfafa Zaman Lafiya Afrika
Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi Afrika
APC Ta Bayyana Abba Yusuf A Matsayin Halastaccen Ɗan Takara Bayan Cika Sharudda Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Kira Ga Haɗin Kai Domin Bunƙasa Maɗaba’u
  • Mataimakin Shugaban kasar Najeriya Ya Kaddamar Da Taron Zuba Jari A Jihar Jigawa
  • Uwargidan Shugaban Ƙasar Najeriya Ta Ƙaddamar Muhimman Ayyuka A Jihar Jigawa
  • Gwamnatin Najeriya Ta Fara Aikin Babbar Hanyar Da Za Ta Haɗa Jihohin Arewa
  • Gwamnatin Benue Da MACBAN Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Marigayi Ardo Risku Mohammed

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Uefa Ta Zabi Artan, Ya Jagoranci Wasan Cin Kofin Uefa Super Cup Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Yakin Iran Da Isra’ila Da Amurka Zai Shafi Kasashen Afirka – Masana Afrika
  • FRSC Gombe: Hatsarin Mota Ya Yayi Ajalin Mutane 38 Ya Jikkata Fiye Da 218 A Wata Ɗaya Najeriya
  • Kasar Gabon Ta Nemi Tallafin Asusun Bada Lamuni Na IMF Afrika
  • Ronaldo Da Messi Ka Iya Hadu A Gasar Cin Kofin Duniya: Ta Ya Ya ? Wasanni
  • Kasar Saudiya Zata Cika Azumi Talatin Kimiya
  • Kasar Iceland Ta Kauracewa Bikin Gasar Wakokin Shekara Mai Zuwa Labarai
  • An Kama Masu Fasa Kaurin Gawayi A Malawi Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.