Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Kasashen Yankin Gulf Sun Bada Sanarwa
Published: March 28, 2026 at 8:23 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Kasashen larabawa da suke yankin Gulf, sun gayawa Amurka cewa, duk wata yarjejeniya da Iran, kada ya tsaya wajen kawo karshen yakin kawai, tilas ya kunshi matakai na har abada da za su gurgunta karfinta ta fuskar makamai masu linzami, da jiragen drones, da kuma, tabbatar kasar ba zata sake hana zirga zirgan jiragen ruwa a mashigin ruwa na Hormuz ba. Kamar yadda wasu majiyoyi hudu daga kasashen da suke yankin Gulf suka fada.

Shugaba Donald Trump, ya kara wa’adin da ya baiwa Iran ta bude mashigin ruwan Hormuz, inda ta nan ne kashi 20 cikin dari na mai da iskar gas da duniya take amfani da shi suke bi, ko kuma Amurka ta afkawa cibiyoyin makamashin Iran.

Amma babbar ayar tambaya da masu tsare tsare da kwararru a yankin suke fuskanta shine abunda zai biyo bayan kawo karshen yakin, wace irin makoma ce yankin zai fuskanta, kamar yadda majiyoyin hudu suka shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Jami’an kasashe da suke yankin na Gulf da Iran take harba makamai a kansu a yayin wannnan yakin hadin guiwar Amurka da Isra’ila akan Tehran, suna gayawa hukumomi a Washington cewa, Iran bata bar musu wata dama ko hanyar sulhu ta fuskar Diflomasiyya ba.

Afrika, Amurka, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: APC Ta Yi Babban Taron Amincewa Da Shugabannin Jam’iyyar Ba Hamayya
Next Post: Farashin Mai Ya Tashi A Kasuwannin Duniya

Karin Labarai Masu Alaka

Masu Luwadi Na Fuskantar Tara Da Daurin Shekaru 20 A Nijar Afrika
Afirka Ta Kudu Ta Bayyana Yadda Aka Yaudari ‘Yan Kasar Ake Tilasta Musu Ayyukan Bauta Afrika
‘Yan Tawayen Houthi Sunkai Hari Isra’ila Afrika
Matasa Sun Sayawa Ferfesa Pantami Fom Din Takarar Gwamnan Gombe Afrika
An tura tsohon ministan Ilimin Nijar gidan yari saboda zargin aikata fyade ga wata daliba. Afrika
Gwamnonin Arewa Sunyi Allah Wadai Da Matsalar Tsaro A Shiyar Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Sojoji 15 Da Wasu Fararen Hula A Benin Afrika
  • Bangladesh Tasamu Rangwamen Harajin Da Amurka Ta Kakaba Mata Labarai
  • Maikaba Ya Yi Murabus A Matsayinsa Kocin Wikki Tourist FC Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Shugaban Kasar Uganda Yana Kokarin Mayar Da Mulkin Kasar Na Gado Labarai
  • Jami’yar ADC A Najeriya Ta Kori Nafiu Bala Afrika
  • Hukumar IMF Tana Naziri Domin Kara Bada Lamuni Ga Kasar Zambiya Afrika
  • Jami’ar Tarayya A Gombe Ta Karyata Harin ‘Yan Bindiga Najeriya
  • Sarkin Gombe Ya Ziyarci Gwamna Inuwa Yahaya Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.