Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Muhimmin Sako Ga Alhazai Dake Kasar Saudiya Afrika
  • Tinubu Ya Lashe Zaɓen Fidda Gwanin APC Da Kuri’u Miliyan 11 Afrika
  • Tsohuwar Jarumar Kannywood Wasila Ismail Ta Rasu Afrika
  • Za’a Fassara Hudubar Arfa Da Harshen Hausa Afrika
  • An Kamallah Jigilar Alhazain Najeriya Domin Hajjin 2026 Afrika

Fafaroma Leo Yayi Allah Wadai Bisa Karuwar Yake Yaken Gabas Ta Tsakiya
Published: March 30, 2026 at 9:31 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Fafaroma Pope Leo ya bayyana a ranar Lahadi cewa Allah ba ya karɓar addu’o’in shugabannin da ke fara yaƙe-yaƙe kuma “hannuwansu cike suke da jini,” a wata magana mai ƙarfi da ya yi yayin da yaƙin Iran ya shiga wata na biyu.

A dai-dai lokacin da yake jawabi ga dubban mutane a dandalin St. Peter’s Square a ranar Palm Sunday bikin da ke buɗe mako mai tsarki kafin Easter ga Mabiya darikar Katolika biliyan 1.4 miliyan a duniya Fafaroman ya bayyana rikicin a matsayin “mummuna ƙwarai,” yana mai cewa ba za a iya amfani da Yesu don halatta wani yaƙi ba.

Ya ce: “Wannan shi ne Allahnmu: Yesu, Sarkin Salama, wanda ke ƙin yaƙi, kuma babu wanda zai iya amfani da shi don halatta yaƙi.” Leo, wanda shi ne Fafaroma na farko daga Amurka, ya faɗa wa taron jama’a a cikin hasken rana mai ƙyalli.

Ya ƙara da cewa: “(Yesu) ba ya sauraron addu’o’in waɗanda ke tayar da yaƙi, sai dai yana ƙin su, yana cewa: ‘Ko da kuna yawaita addu’a, ba zan saurara ba: hannuwanku cike suke da jini,’” yana mai ambaton wani sashe na Littafi Mai Tsarki.

Fafaroman bai ambaci sunan wani shugaba na duniya kai tsaye ba, amma ya ƙara tsananta suka kan yaƙin Iran a makonnin baya-bayan nan.

Amurka, Labarai, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Pakistan Zata Karbi Tattaunawar Rikicin Gabas Ta Tsakiya
Next Post: Wani Jirgin Sama Ya Karya Dokar Hana Zirga Zirga

Karin Labarai Masu Alaka

Mayakan RSF Sun Zafafa Kai Hare Hare Da Jirgi Maras Matuki A Sudan Labarai
Donald Trump Yace Basu Cimma Matsaya Da Benjamin Natanyahu Ba Afrika
Shugaban Ukraine Ya Tattauna Da Trump Akan Zaman Lafiya Amurka
Kasar China Tana Cigaba Da Nuna Fin Karfi Ga Kasar Taiwan Labarai
An Gudanar Da Jana’izar ’Yan Jaridan Da Suka Rasu A Jihar Gombe Labarai
Thailand Da Cambodia Sun Fara Tattauunawa Kan Batun Tsagaita Wuta Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Muhimmin Sako Ga Alhazai Dake Kasar Saudiya
  • Tinubu Ya Lashe Zaɓen Fidda Gwanin APC Da Kuri’u Miliyan 11
  • Tsohuwar Jarumar Kannywood Wasila Ismail Ta Rasu
  • Za’a Fassara Hudubar Arfa Da Harshen Hausa
  • An Kamallah Jigilar Alhazain Najeriya Domin Hajjin 2026

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Afirka Ta Kudu Ta Kama ‘Yan ƙasar Kenya Su Bakwai Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Thailand Da Cambodia Sun Fara Tattauunawa Kan Batun Tsagaita Wuta Labarai
  • Jamhuriyar Dimokraɗiyya Kwango Ta Bukaci Rwanda Ta Daina Marawa ‘Yan Tawayen M23 Baya Afrika
  • An Garkame Wani Babban Soja A Kasar Australiya Afrika
  • Sojoji Zasu Taimakawa ‘Yan Sanda Wajen Yaki Da Mugayen Ayyuka Labarai
  • Kurdawa Sun Gargadi ‘Yan Uwansu Game Da Alaka Da Amurka Wajen Yakar Iran Afrika
  • An Kai Shugaban Kasar Venezuela Kotu Amurka
  • Dakarun Gwamnatin Kasar Sham Tayi Mamaya Zuwa Gabashin Kasar Labarai
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.