Wani dan bindiga ya bude wuta ya harbi wasu dakarun tsaron cikin gida su biyu daga Jihar West Virginia da aka girka a nan Washington DC, dab da fadar White House, a wani lamarin da magajiyar garin birnin Washington ta bayyana a zaman hari na gangan a kan sojojin.
Darektan hukumnar binciken manyan laifuffuka ta tarayya, Kash Patel, da magajiyar garin birnin Washington, Muriel Bowser, sun ce dakarun suna kwance a asibiti, rai a hannun Allah.
Irin wannan farmaki na ba-saban ba a kan dakarun tsaron cikin gida yana zuwa a daidai lokacin da ake ta ci gaba cacar baki kan girka irin wadannan dakaru a nan Washington da wasu birane, inda aka yi wata da watanni ana shigar da kararraki a kotuna da yin zaga-zanga kan yadda gwamnatin Trump take amfani da sojoji don takalar abinda ta kira matsalar aikata laifuffuka.
Shi ma wanda ake zargin cewa dan bindigar ne, an harbe shi kuma na kama shi, amma ana jin rauninsa ba mai tsanani ba ne.
Nan da nan gwamnatin Mr. Trump ta bada umurnin da a kara turo karin dakarun tsaron cikin gida dari biyar (500) zuwa nan Washington.


