Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Jiragen Ruwa Suna Biyayya Ga Dokar Hana Ketare Ruwa
Published: April 14, 2026 at 8:43 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Kwana daya da fara hana jiragen ruwa shiga ko fita daga tashoshin ruwan Iran, dakarun Amurka suka ce babu jirgin ruwa ko daya daya tsallake shinge da suka kafa, jiragen ruwa shida sun bi umarni suka juya, wannan shine bayani na farko da aka samu tun bayan da shugaban Amurka Donald trump, ya bada umarnin killace tashoshin ruwan Iran, sakamakon rushewar zaman shawarwari da kasashen biyu suka yi a Pakistan.

Sojojin na Amurka suka ce wannan mataki ya shafi jirage ne da suke kokarin shiga tashoshi a gaban ruwan Iran da Oman.

Rundunar mayakan na Amurka ta ce fiye da sojojin Amurka dubu 10, jiragen yaki na ruwa masu yawa da masu tashi sama ne suke aiwatar da dokar hana zirga zirga zuwa tashoshin ruwan na Farisa.

Sanarwar da cibiyar kula da yake yake ta Amurka ta bayar tace dokar ta shafi dukkan jiragen ruwa daga ko wace kasa ba tare da wani zabi ba.

Sanarwar ta ci gaba da cewa hana zirga zirgar zai shafi illahirin tashoshin ruwan Iran, amma za’a kyale jirage dauke kayan abinci, magunguna da wasu muhimman kayayyaki su wuce bayan da aka duba abunda suke dauke dashi.

Masana sun gayawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa matakin yana iya janyo martani daga Iran, da zai iya kara dagula lamari kan yarjejeniyar tsagaita wuta maras tabbas.

Amurka, Labarai, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Gwamnatin Najeriya Tace A Maboyar ‘Yan Ta’adda Aka Kai Harin Jilli
Next Post: Papa Roma Leo Yayi Gargadi Game Da Rushewar Dimokraɗiyya

Karin Labarai Masu Alaka

‘Yan Sanda A Tsibirin Bahamas Sun kama Mijin Wata Ba Amurkiya Amurka
Ingila, Hauhawar Farashi Yayi ƙasa Sosai Labarai
Shugaba Trump Yayi Barazanar Tura Sojoji Ga Masu Zanga Zanga Amurka
Ambaliyar Ruwa Yayi Ajalin Mutane A Nairobi Afrika
Kasar Habasha Ta Cimma Matsaya Da Masu Binta Bashi Afrika
Gwamnatin Jihar Yobe: Ana Cin Zarafin Fursunoni A Gidan Gyaran Halin Potiskum Tsaro

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Rikici Ya Barke A Kano Bayan Kashe Wani Matashi Da Ake Zargi Da Kashe Ladani Najeriya
  • Shugabannin Kiristoci Sun Taya Musulmi Murnar Sallah Domin Ƙarfafa Zaman Lafiya Afrika
  • Iran Ta Karyata Tattaunawa Da Washington Afrika
  • An Gudanar Da Zanga-Zanga A Kasar Somaliya Labarai
  • Gwamnatin Najeriya Ta Karyata Raɗe-Raɗin Canza Sunan Kasar Da Soke Shari’a A Arewa Afrika
  • An Canza Shugabannin Hukumar Hakar Ma’adanai A Congo Labarai
  • Babban Sakataren MDD Yayi Allah Wadai Da Matakin Soja A Gabas Ta Tsakiya Afrika
  • Angano Gawar Wani Dan Myanmar A Arewacin New York Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.