Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Sojoji Sun Dakile Harin ’Yan Ta’adda a Kukareta
Published: April 23, 2026 at 7:43 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

​Rundunar sojin hadin gwiwa ta Operation Hadin Kai (OPHK) da ke lura da shiyya ta biyu a Najeriya ta yi nasarar fatattakar wani gagarumin hari da ’yan ta’adda suka kai yankin Kukareta a daren Laraba wayewar Alhamis.

​Harin, wanda aka fara shi jim kadan bayan tsakar dare zuwa misalin karfe 3:00 na asuba, ya gamu da tirjiya daga dakarun soji wadanda suka yi martani, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa bayan sun tafka asara mai yawa.
​
A cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na rundunar, Laftanar Kanar Sani Uba ya fitar a ranar 23 ga watan Afrilu, 2026, ya bayyana cewa sojoji sun yi nasarar kashe ’yan ta’adda 24 a yayin artabun.

​Haka kuma, binciken da sojoji suka gudanar a fagen daga bayan kura ta lafa ya kai ga gano dimbin makaman da ’yan ta’addan suka bari, wadanda suka hada da ​Bindigogi kirar AK-47 guda 18 da wasu manyan bindigogi na GPMG guda 3, ​Bindigogin kakkabo jiragen sama (PKT) guda 2 da bututun harba bama-bamai na RPG guda 3 da na Mortar guda 2, ​Guruneti (Hand grenades) guda 4 da kuma dimbin alburusai.

Sanarwar ta kara da cewa sojoji biyu ne suka samu raunuka a lokacin musayar wuta, kuma tuni aka duba lafiyarsu inda suke cikin yanayi mai kyau. Kazalika, wata motar yaki ta sojoji (Tank) guda daya ta samu matsala bayan tayoyinta sun fashe a lokacin da take kai dauki.

A halin yanzu, sojoji na ci gaba da bin sawun ’yan ta’addan da suka tsere da raunuka, inda aka ga alamun jini da kayayyakin magunguna a hanyoyin da suka bi yayin gudun ceton rai.

​Wannan nasara dai ta kara tabbatar da irin shirin da dakarun soji suke da shi na murkushe duk wani yunkuri na ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas, inda rundunar ta lashi takobin ci gaba da matsa lamba har sai ta kawo karshen ayyukan ta’addanci a yankin baki daya.

Afrika, Labarai, Najeriya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Tawagar Masu Yi Wa Maniyyata Hidima Za Ta Tashi Zuwa Saudiyya
Next Post: Akwai Bukatar APC Tayi Gyare-Gyare Kafun Zabe

Karin Labarai Masu Alaka

NDPHC Ta Yi Alkawarin Tallafa Wa Gombe Wajen Inganta Wutar Lantarki Afrika
Kotu A Kasar Tunisiya Ta Daure Wani Babban Dan Kasuwa Da Wasu ‘Yan Majalisa Afrika
Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
Hukumar NAPTIP Ta Kubutar Da Yara 11 Daga Hannun Masu Safara Mutane Labarai
Kungiyoyin Mata A Jihar Filato Sunyi Gangamin Samun Jagorancin Siyasa Afrika
Ukraine Da Syria Zasuyi Haɗin Gwiwar Tsaro Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Hukumar Upper Benue Zata Inganta Noma A Dadinkowa Afrika
  • Shirin Safe 0500 UTC Yau Juma’a 11.21.2025 Rediyo
  • Farfesa Inuwa Ja’afaru Yakarbi Ragamar Shugabancin Jami’ar Kashere Labarai
  • Madrid, Arsenal Da Chelsea Sun Fara Zaurancen Dan-Wasa Kenan Yildiz Wasanni
  • Kasar Faransa Ta Karyata Cire Afirka Ta Kudu Daga G7 Afrika
  • 3G Taskforce Ya Dasa Bishiyoyi Don Kare Muhalli A Gombe Afrika
  • Jarman Deba Ya Kada Senata Goje A Zaben Fidda Gwani Afrika
  • Arsenal Ta Doke Manchester City 3-0, Ta Ɗauki Kofin Community Shield Wasanni
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.