Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Gwamnatin Najeriya Ta Jinjinawa Saudiya
Published: April 27, 2026 at 7:42 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta jinjina wa Masarautar Saudiyya bisa samar da gurbin karatu na kyauta ga daliban Najeriya su 50 domin karantar fannin man fetur da ma’adanan kasa.

Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan yayin da ya karbi bakuncin Jakadan Saudiyya a Najeriya, Yousef Bin Mohammed Al-Balawi, wanda ya ziyarce shi a ofishinsa da ke Abuja ranar Litinin, 27 ga watan Afrilu, 2026.

Ministan ya bayyana cewa wannan tallafin karatu ya zo daidai da burin gwamnati na bunkasa ilimi da kwarewa a fannonin da suka shafi tattalin arzikin kasa. Ya ce wannan ba gurbin karatu ba ne kawai, a’a, wani babban jari ne da za a zuba wa matasan Najeriya.

“Wannan mataki zai samar da kwararrun da Najeriya ke bukata a masana’antun man fetur da ma’adanan kasa,” in ji Ministan.

Ya kuma kara da cewa an tsara shirin ta yadda dalibai 50 za su rika amfana a duk shekara, wanda hakan zai tabbatar da dorewar shirin na dogon lokaci.

A nasa bangaren, Jakada Al-Balawi ya sanar da cewa gurbin karatun ya fito ne daga Jami’ar Man Fetur da Ma’adanai ta King Fahd (KFUPM). Ya bayyana cewa tallafin ya hada da Biyan kudin makaranta (Tuition), Tikitin jirgin sama na zuwa da dawowa, Wajen kwana kyauta, da Alawus din dake shiga hannu a kowane wata.

Jakadan ya jaddada cewa wannan kokari na nuna kyakkyawar alakar dake tsakanin kasashen biyu, yana mai cewa Saudiyya da Najeriya ginshikan tattalin arziki ne a yankunansu wadanda ke da damar bunkasa huldar kasuwanci a tsakaninsu.

Ministan ya kuma yi amfani da damar wajen bayyana jimamin Najeriya game da takaddamar dake faruwa a yankin tekun Gulf, inda ya mika sakon goyon bayan Najeriya ga kasar Saudiyya. Ya bayyana fatan samun zaman lafiya da kuma daidaita duk wata matsala ta hanyar diflomasiyya.

A karshen zaman, Ministan ya tabbatar wa jakadan cewa Najeriya za ta gaggauta aiwatar da sauran yarjeneniyoyin da aka kulla da Saudiyya, ciki har da wadanda suka shafi fannin yada labarai da sauran sassa.

Ziyarar ta samu halartar Babban Sakataren ma’aikatar, Dr. Binyerem C. Ukaire, da wasu manyan daraktoci na ma’aikatar yada labaran.

Afrika, Kimiya, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: UNICEF Ta Tallafawa Jihar Bauchi Da Babura
Next Post: Tinubu Ya Sayi Fom Din Takarar Shugaban Kasa

Karin Labarai Masu Alaka

Eziekel Gomos Ya Zamo Babban Daraktan Sakatariyar Zauren Gwamnonin Arewa Najeriya
Indiya Da Brazil Sun Kulla Yarjejeniyar Cinikayya Afrika
‘Yan Gudun Hijira A Kasar Libya Suna Fuskantar Cin Zarafi Afrika
Shugaban Kasar Iran Ya Bayyana Samun Sakamako Mai Kyau A Tattaunawa Da Amurka Amurka
Tinubu Ya Jaddada Aniyar Rage Tsadar Rayuwa Da Samar da Ayyukan Yi Afrika
Malaman Addinin Musulunci Da Kirista Sunyi Bikin Cika Shekara 15 Na Iftar A Najeriya Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shirin Dare 2030 UTC Yau Juma’a 11.21.2025 Rediyo
  • Gwamnatin Gombe Zata Inganta Samar Da Wuta Wajen Amfani Da Hasken Rana Kimiya
  • Zamu Hana Wasu ‘Yan-Najeriya Visa Shiga Amurka Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Kasar Spain Ta Rufe Sararin Saman Kasar Amurka
  • Amurka Ta Janye Sojojinta Daga Gabas Ta Tsakiya Amurka
  • Kotun Daukaka Kara A Faransa Zata Tabbatar Da Hukuncin ‘Yan Jam’iyyar Ra’ayin Rikau Labarai
  • Dakarun Tsaron Ruwan Amurka Sunfara Killace Hanyoyi Amurka
  • ‘Yan Ta’adda Sun Kashe ‘Yan Sanda A Jihar Katsina Najeriya
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.