Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

Likitoci Masu Neman Kwarewa Zasu Shiga Yakin Aiki
Published: June 7, 2026 at 1:31 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: June 7, 2026

Ƙungiyar likitoci masu neman kwarewa ta Nijeriya, wato Nigerian Association of Resident Doctors (NARD), ta yi barazanar shiga yajin aiki idan gwamnati ba ta ɗauki matakan da suka dace ba wajen dakile cin zarafi da ake kai wa ma’aikatan lafiya a faɗin ƙasar.

Ƙungiyar ta bayyana cewa aƙalla manyan cibiyoyin lafiya 17 sun fuskanci hare-hare kan likitoci, ma’aikatan jinya da sauran ma’aikatan lafiya cikin shekara guda da ta gabata.

Ta ce sama da kashi 90 cikin 100 na waɗanda abin ya shafa mambobinta ne, inda suka gamu da raunuka da asarar dukiya.

NARD ta ce idan har zuwa ƙarshen taronta na shekara ba a ɗauki matakai masu gamsarwa ba wajen hukunta masu aikata irin waɗannan cin zarafi ba, ba za ta iya tabbatar da zaman lafiya a fannin kiwon lafiya ba bayan taron.

Ƙungiyar ta koka da cewa galibin waɗanda aka kai wa hari suna samun wasiƙar neman afuwa kawai daga masu laifi, ba tare da an hukunta su yadda ya kamata ba. Ta kuma zargi hukumomi da gaza gurfanar da masu laifin, lamarin da ke ƙara ƙarfafa masu aikata irin waɗannan laifuka.

NARD ta ce asibitocin da ya kamata su kasance wuraren ceto rayuka suna sauyawa zuwa wuraren tashin hankali, inda cin zarafi ta baki ya rikide zuwa duka, lalata dukiyoyi, kutsawa ɗakunan hutun likitoci da kuma yi musu barazana da makamai.

Ƙungiyar ta jaddada cewa rayukan likitoci da sauran ma’aikatan lafiya suna da muhimmanci, tana mai kira ga gwamnati da hukumomin tsaro su ɗauki matakan gaggawa domin kawo ƙarshen wannan matsala.

Afrika, Kiwon Lafiya, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Gwamnan Gombe Ya Yaba Da Hikima Da Jagorancin Sarkin Gombe A Shekaru 12 Na Jagoranci
Next Post: Iran: Za A Gudanar Da Jana’izar Khamenei Bayan Kwanaki Goma Na Muharram

Karin Labarai Masu Alaka

Mun Kwato Kimanin Naira Biliyan 40 Na Badakala A Tsawon Shekara Daya Labarai
Za’ayi Auren Zawarawa Dubu Uku A Kano Afrika
Muhimmin Sako Ga Alhazai Dake Kasar Saudiya Afrika
Amurka Da Iran Sun Tattauna A Kasar Pakistan Afrika
Kasar Colombia Tare Da Amurka Zasu Fitar Da Man Venezuela Labarai
Indonesia Zata Kafafa Rundunar Kiyaye Zaman Lafiya A Gaza Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • An Kaddamar Da Jigilar Maniyyata Aikin Hajji A Abuja Afrika
  • ‘Yan Kasar Cuba Sunyi Zanga Zanga A Ofishin Jakadancin Amurka Amurka
  • ‘Yan Sandan Najeriya Sunyi Nasarar Hallaka ‘Yan Ta’adda A Katsina Afrika
  • Gombe Ta Zo Ta Biyu Wajen Aiwatar Da Shirin L-PRES Afrika
  • Rangadin Ayyukan Tinubu Ya Kai Tawaga Zuwa Kano Northern Bypass Afrika
  • An Kaiwa Sojojin Ghana Hari Da Makami Mai Linzami Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • Najeriya Da Amurka Sun Amince Su Haɗa Kai Don Inganta ’Yancin Addini Da ƙarfafa Tsaro A Nijeriya Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.