Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Dakarun Sojin Najeriya Sun Kashe Yan Kungiyar Lakurawa
Published: June 16, 2026 at 3:37 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Dakarun Soji na Sashe na biyu na oferashan FANSAN YAMMA da ke aiki a jihar Kebbi sun kwato tarin manyan makamai da kuma bama-bamai (IEDs), a wani ci gaba da ƙoƙari da nufin kawar da ta’addanci da sauran ayyukan miyagun laifuka a yankin Arewa maso Yamma.

An gudanar da wannan farmaki ne a ranar 14 ga Yuni, 2026, a yankin Dogon Daji da ke Ƙaramar Hukumar Dandi ta jihar. A yayin farmakin, jaruman dakarun sun yi amfani da ƙarfin wuta mai yawa wajen murƙushe ƙungiyar ‘yan ta’addan Lakurawa, lamarin da ya tilasta musu tserewa daga wajen.

A ci gaba da bin sawun ‘yan ta’addan da suka gudu ya kai ga gano da kwato dimbin makamai, bama-bamai da kayan aiki da suka bari a baya yayin tserewar su.

Mai magana da yawun rundunar, Laftanar Kanal Olaniyi Osoba, ya ce kayan da aka kwato daga sansanin ‘yan ta’addan sun haɗa da bututun harba roka (RPG), rokokin yaƙi da dama da ake sama bututun harba roka (warheads), bama-bamai na gida (IEDs) masu yawa, babura guda biyu da ‘yan ta’addan ke amfani da su wajen kai hari, caja na batura, da wasu kayayyakin su na kashin kai.

Ya ƙara da cewa dakarun sun kammala wannan fafatawa lafiya lau, ba tare da samun asara ko jikkata ba.

Ya kuma jaddada cewa wannan nasara na nuna ƙudirin rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Yamma, oferashan FANSAN YAMMA, na rushe hanyoyin ‘yan ta’adda da ‘yan fashi da makami a yankin.

A cewarsa, Rundunar Sojin Najeriya za ta ci gaba da matsa lamba kan wadannan miyagun, tare da hana su damar gudanar da ayyukansu domin tabbatar da tsaro da lafiyar al’umma masu bin doka.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sauran Duniya, Tsaro

Post navigation

Previous Post: Shugaba Tinubu Ya Yabawa Dakarun Tsaro Bisa Ceto Matar Marigayi Janar Rabe
Next Post: Rashin Hanya da Asibiti Ya Jawo Asarar Rayuka A Jihar Gombe – Sarkin Gargajiya

Karin Labarai Masu Alaka

Ahmed Gara Ya Kaddamar da Kofin Sarkin Gombe, Ya Jaddada Bunƙasa Matasa Afrika
Matatar Man Dangote Zata Wadatar Da Najeriya Da Makota Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
Gwamnatin Najeriya Ta Jinjinawa Saudiya Afrika
Gwamnan Gombe Ya kori Wasu Hadimansa Bisa Cin Zarafin Kansila Najeriya
Fintiri: Zamu Maida Jihar Adamawa Sabuwar Duniya Labarai
Hukumar Zaben Najeriya Ta Sanar Da Ranar Zaben Shugaban Kasa Labarai

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Rashin Tsaro: Gwamnati Ta Bada Umarnin Daukar Ma’aikata Sama Da 94,000 Najeriya
  • Da Arzikin Mu: Bamu Ba Bautawa Turawan Yamma Afrika
  • Dubban Mutane Sunyi Zanga-Zanga A Kasar Australia Afrika
  • Jakadan Amurka A Poland Ya Yanke Hulda Da Kakakin Majalisar Kasar Labarai
  • Rasha Takai Hari Ukraine Da Jirgi Marar Matuki Afrika
  • Baitul Malin Amurka Zata Bawa Venezuela Da Cuba Damar Sayar Da Mai Amurka
  • ‘Yansandan Uganda Sun Tsare ‘Yar Fafutukar Kare Hakkin Bil’adama Sarah Bireete Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Gwamnatin Trump Tana Cigaba Da Korar Baki Daga Amurka Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.