Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Makokin Ashura: An Gudanar Da Taron Tunawa Da Aliyul Asghar A Gombe
Published: June 20, 2026 at 7:15 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Kungiyar ‘yan uwa Musulmi Almajiran Sayyid Ibrahim Yaqub El-Zakzaky (H) a jihar Gombe sun shiga rana ta uku na gudanar da zaman makokin Ashura, domin tunawa da shahadar Imam Hussain (AS) da iyalan gidan Manzon Allah (SAW) a filin Karbala, lamarin da ya faru a shekara ta 61 bayan hijira.

A ranar ta uku, an gudanar da wani shiri na musamman domin tunawa da Aliyul Asghar (AS), jaririn Imam Hussain (AS), wanda ya yi shahada a lokacin yaƙin Karbala.

Da yake gabatar da jawabi a wajen taron, Shugaban ‘yan uwa Musulmi a Gombe Sheikh Muhammad Abbari ya yi cikakken bayani kan yadda Aliyul Asghar ya yi shahada, tare da bayyana darussan sadaukarwa, juriya da tsayin daka da ake koya daga wannan tarihi.

Shehin malamin ya jaddada muhimmancin bin tafarkin Imam Hussain (AS) wajen kare gaskiya da adalci, yana mai kira ga mabiya da su kasance masu jajircewa a gaban zalunci da danniya.

Ya kuma yi bayani kan ƙa’idojin yaƙi a Musulunci, inda ya ce abin da aka yi wa Aliyul Asghar ya saɓa wa dokoki da ka’idojin yaƙi da addinin Musulunci ya tanada.

A yayin taron, iyaye masu jarirai sun ɗaga ‘ya’yansu a matsayin alamar tunawa da yadda Imam Hussain (AS) ya ɗaga jaririnsa a filin Karbala lokacin da yake neman a ba shi ruwa.

Mahalarta taron sun bayyana cewa wannan alama ce ta nuna biyayya ga koyarwar Imam Hussain (AS) da kuma ci gaba da bin tafarkin gwagwarmayar tabbatar da gaskiya da adalci.

An gudanar da taron cikin yanayi na jimami, addu’o’i da wa’azi, yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen makokin Ashura a sassa daban-daban na jihar Gombe.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Nishadi, Sana'o'i, Sauran Duniya

Post navigation

Previous Post: Rashin Hanya da Asibiti Ya Jawo Asarar Rayuka A Jihar Gombe – Sarkin Gargajiya
Next Post: Bayan Shekaru Biyar, Rundunar ‘Yan Sandan Gombe Ta Gano Motar da Aka Sace A Fatakwal

Karin Labarai Masu Alaka

Rundunan  ‘Yan Sandan Jihar Bauchi, Ta Miƙa Miyagun Ƙwayoyi Da Ta Kama Wa NDLEA. Labarai
Gwannatin Jihar Kebbi Ta Arawa Maniyyata Kuɗin Aikin Hajji 2026, Labarai
Jami’an tsaro sama da dubu biyar ne zasuyi aikin tabbatar da tsaro Alokacin bikin karamar sallah a Jihar Nejan Najeriya. Najeriya
Kotun Uganda Tayi Watsi Da Karar Hukumomin Kasar Afrika
Matatar Man Dangote Ta Kara Yawan Mai Dake Zuwa Kasashen Afirka Afrika
An Kai Hari Babbar Tashar Iskar Gas A Iran Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • An Bukaci Matasa Su Taka Gagarumar Rawa Wajen Gina Zaman Lafiya A Arewa Maso Gabas Afrika
  • Gwamnatin Bauchi: Ba Zamu Bude Makarantu Ba Sai 2026 Labarai
  • Shugaba Donald Trump Yabada Umarnin Hana Jiragen Dakon Mai Shiga Venezuela Amurka
  • Salmanu: Ci Gaban Wikki Tourist FC Shine A Gaba Na Wasanni
  • Togo Ta Kama Tsohon Shugaban Kasar Burkina Faso Saboda Kitsa Juyin Mulki Afrika
  • INEC Mayar Da Lokacin Zaɓen 2027 Kafin Azumi Najeriya
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi Afrika
  • Iran Ta Harbo Jiragen Yakin Amurka Biyu Amurka
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.