Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi Afrika
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19 Afrika
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027 Afrika
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki Afrika
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko Afrika

An Binne Gawar Tsohon Shugaban Sashen Hausa Na VOA, Leo Keyen
Published: July 4, 2026 at 4:33 PM | By: Aliyu Bala Gerengi | Updated: July 4, 2026

An binne gawar tsohon shugaban Sashen Hausa na Gidan Rediyon Muryar Amurka (VOA), Leo Keyen, yayin da ‘yan’uwa, abokan aiki da abokan arziki suka yi masa bankwana tare da bayyana shi a matsayin ƙwararren ɗan jarida, shugaba nagari, kuma mai jajircewa wajen bunƙasa aikin jarida da raya matasa.

Marigayi Leo Keyen ya rasu ne a ranar 22 ga Yunin 2026, yana da shekaru 70 a duniya, bayan ya shafe kusan shekara goma sha ɗaya yana fama da cutar Parkinson’s Disease.

Da yake jawabi, ɗan’uwan marigayin, Injiniya Noel Keyen, ya ce rasuwar ta yi wa iyali da abokansa babban rashi, amma sun amince da hukuncin Allah.

Marigayi Leo Keyen ya yi aiki a cibiyoyin yaɗa labarai da dama, ciki har da NTA da JIB, sannan ya kasance Daraktan Yaɗa Labarai na Jam’iyyar PDP ta ƙasa a zamanin marigayi Solomon Lar. Haka kuma, ya taba zama Babban Daraktan Gidan Rediyo da Talabijin na Jihar Filato (PRTV) sau biyu.

Daga shekarar 2011 zuwa 2018, Leo Keyen ya jagoranci Sashen Hausa na VOA, inda ya faɗaɗa ayyukan rediyo, talabijin da kafafen yanar gizo, lamarin da ya ƙara yawan masu sauraro da masu kallo a Najeriya, Nijar, Kamaru, Chadi da sauran ƙasashe.

Wasu daga cikin shirye-shiryen da ya assasa sun haɗa da Dandalin VOA, Taskar VOA da kuma Tattaunawa, waɗanda suka mayar da hankali kan siyasa, shugabanci da harkokin tsaro.

Tsohon Shugaban Gidauniyar Horas da Ma’aikata ta ITF, Sir Joseph Ari, ya ce ƙwarewar Leo Keyen ta taimaka wajen samar da ingantattun labarai da shirye-shiryen da suka amfani al’umma.

Shi ma tsohon abokin aikinsa a VOA, Malam Sahabo Imam Aliyu, ya bayyana marigayin a matsayin shugaba mai adalci da nagarta, yayin da Hajiya Madina Dauda Nadabo ta ce Leo Keyen mutum ne da bai nuna bambanci tsakanin ma’aikatansa.

Baya ga aikin jarida, marigayin ya kasance mai ƙarfafa gwiwar matasa wajen shiga harkokin kasuwanci da dogaro da kai.

A nasa jawabin, Hon. Kefiano Kefas Ropshik ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da kula da iyalan marigayin tare da tuna gudunmawar da ya bayar ga ci gaban aikin jarida.

Marigayi Leo Keyen ya rasu ya bar matarsa guda ɗaya, ‘ya’ya huɗu da jikoki uku. Allah Ya jikansa da rahama. Ameen.

Ga Rahoton Wakiliyar GTA Hausa Amurka Ke Magana Zainab Babaji Daga Jos

https://gtahausa.com/wp-content/uploads/2026/07/AUD-20260704-WA0020.mp3
Afrika, Labarai, Najeriya, Rumbun Hotuna

Post navigation

Previous Post: ‘Yan Jaridar Gidan Gwamnatin Bauchi Sun Kammala Taron Horo Kan Fasahar Sadarwar Zamani
Next Post: Rangadin Ayyukan Tinubu Ya Kai Tawaga Zuwa Kano Northern Bypass

Karin Labarai Masu Alaka

Babu Alamar Tsagaita Wuta A Yakin Gabas Ta Tsakiya Afrika
Kotu Ta Bada Belin Nasiru El Rufai Afrika
Rikici Ya Lafa A Kasar Iran Bayan Daukar Matakai Labarai
Gwamnatin Tarayya Ta Cire Sharadin Rubuta UTME Ga Masu Neman Shiga Kwalejojin Ilimi Afrika
Sabunta Manhajar Ilimi A Duk Matakai Nasara Ce! Najeriya
Sakamakon Yakin Gabas Ta Tsakiya Kowacce Gangar Mai Ta Haura Dala 100 Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • ’Yan Sandan Gombe Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Da Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
  • Gwamnan Gombe Ya Rantsar Da Sabbin Manyan Sakatarori 19
  • CBCN Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Tinubu A Zaɓen 2027
  • Gwamna Bala Mohammed Ya Miƙa Ta’aziyyar Rasuwar Abdullahi Sule Madaki
  • Al’ummar Wajari Sun Amfana Da Gyaran Cibiyar Kiwon Lafiya Matakin Farko

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Amurka Ta Kwace Jirgin Mai Mallakar Rasha Amurka
  • Anyi Jana’izar Mahaifiyar Nasiru El Rufai A Abuja Afrika
  • Bassirou: Tawagar Senegal Zasu Samu Kyautar Kudi Da Filaye Sakamakon Nasarar Da sukayi AFCON 2025 Wasanni
  • Majalisar Dottijan Najeriya Ta Amince Da Tura Sakamakon Zabe Ta Na’ura Labarai
  • Hukumar ‘Yan Sanda Ta Bukaci Jama’ar Jos Ta Arewa Su Rika Bin Doka Afrika
  • China Ta Yi Kira Da Kasashen Gabas Ta Tsakiya Su Hada Kai Labarai
  • APC Ta Yi Babban Taron Amincewa Da Shugabannin Jam’iyyar Ba Hamayya Afrika
  • Yau Shekaru 60 Da Kisan Gilla Ga Sir. Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.