Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani Afrika
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027 Afrika
  • Najeriya: Gombe ‘Yan Sanda Sun Kammala Bikin Ranar Matasa Da Dasa Itatuwa Domin Makoma Mai Ɗorewa Afrika
  • Inuwa Yahaya Zai Jagoranci Tattara Masu Ruwa da Tsaki Na APC A Arewa Maso Gabashin Najeriya Afrika
  • APC Ta Tsayar Da Usman Maijama’a Kallamu A Zaɓen Cike Gurbi Na Gombe, Kwami Da Funakaye Afrika

Gwamnan Gombe Ya Ƙara Tallafin N148.76bn Domin Aiwatar da Sabon Tsarin Albashi A Jami’ar Gombe
Published: August 20, 2026 at 12:17 PM | By: Aliyu Bala Gerengi

Gwamnan Jihar Gombe kuma Visitor na Jami’ar jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya amince da ƙarin Naira miliyan 148.762 a matsayin tallafin wata-wata ga Jami’ar Jihar Gombe, domin sauƙaƙa cikakken aiwatar da sabon tsarin albashi da aka fi sani da Consolidated Academic Tool Allowance (CATA).

Ƙarin tallafin zai fara aiki ne daga Oktoba 2026, kamar yadda Sakataren Gwamnatin jihar Gombe, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ya bayyana yayin isar da amincewar gwamnan.

Farfesa Njodi ya ce matakin wani ɓangare ne na ƙudurin Gwamna Inuwa Yahaya na magance matsalolin da suka taso sakamakon yarjejeniyar Gwamnatin Tarayya da ASUU ta shekarar 2025.

A cewarsa, ƙarin tallafin da ya kai kashi 56 cikin 100, zai ƙarfafa ikon jami’ar wajen biyan haƙƙoƙin ma’aikatanta tare da samar da isasshen tanadi a kasafin kuɗin jami’ar domin aiwatar da sabon tsarin albashin a cikin Kasafin Ƙarin Kuɗi na 2026.

Ana sa ran Majalisar Dokokin Jihar Gombe za ta duba kasafin ƙarin kuɗin a watan Satumba 2026.
Gwamna Inuwa Yahaya ya kuma umarci shugabancin jami’ar da ya fara dukkan matakan da suka dace domin biyan bashin CATA da aka tara.

Baya ga aiwatar da CATA, gwamnan ya umarci jami’ar da ta samar da hanyoyin cikin gida domin biyan sauran basussukan ma’aikata a hankali, ciki har da bashin ƙarin albashin kashi 25 da kashi 35 cikin 100, mafi ƙarancin albashi, da Earned Academic Allowances.

Gwamnatin ta ce za a biya waɗannan basussuka ne a matakai, tare da la’akari da ɗorewar kuɗaɗen jami’ar da kuma buƙatar ci gaba da gudanar da karatu ba tare da tsaiko ba.

A wani mataki na magance ƙalubalen kuɗaɗen ilimi, Majalisar Dokokin Jihar Gombe ta amince da dokar kafa Asusun Amintaccen Ilimi na Jihar Gombe, wanda ake sa ran fara aiki a watan Oktoba 2026.

An tsara asusun ne domin samar da ingantaccen tsarin samun kuɗaɗen ilimi, musamman ga Jami’ar Jihar Gombe da sauran manyan makarantun gwamnati mallakin jihar.

Gwamnatin ta ce asusun zai ƙara mata damar biyan buƙatun yau da kullum da na raya manyan makarantun jihar, tare da samar da ingantacciyar hanyar kula da jin daɗin ma’aikata da sauran buƙatun jami’o’i.

Gwamnatin jihar Gombe ta kuma yi kira ga Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) da ta yi la’akari da matakan da aka riga aka ɗauka da kuma tabbacin da gwamnati ta bayar na magance matsalolin da suka shafi ƙungiyoyin ma’aikatan ilimi da waɗanda ba na ilimi ba.


Gwamnatin Inuwa Yahaya ta sake jaddada aniyarta ta yin aiki tare da ASUU, shugabancin jami’ar da sauran masu ruwa da tsaki, domin tabbatar da zaman lafiya a masana’antar ilimi, daidaiton harkokin karatu da ci gaba da bunƙasar Jami’ar Jihar Gombe.

Afrika, Labarai, Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu, Najeriya, Sana'o'i, Sauran Duniya, Siyasa

Post navigation

Previous Post: Kuɗaɗen Da EFCC Ta Kwato Za Su Tallafa Wa Shirin Lamunin Karatu
Next Post: NSC Ta Bai Wa Shugabannin NFF Sa’o’i 24 Su Yi Murabus

Karin Labarai Masu Alaka

Shugaba Donald Trump Ya Bayyana Cewa Yana Cikin Masu Zaben Sabon Jagoran Iran Amurka
Jami’ai Daga Amurka Sunce Yakin Amurka Da Iran Zaizo Karshe Amurka
NDLEA Ta Fara Binciken Kwakwaf Akan Wasu ‘Yan Mata Dake Kai Kwaya Gidan Yari Labarai
Ministan Yaɗa Labarai Ya Yi Kira Ga Haɗin Kai Domin Bunƙasa Maɗaba’u Afrika
Jihar Gombe Ta Karbi Bakuncin Taron Tsaro Tsakanin DIG Da Masu Ruwa Da Tsaki Afrika
Tinubu Ya Rantsar Da Shugabar Hukumar FCC Najeriya

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Magoya Bayan Liverpool Sun Bukaci Iraola Ya Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Szoboszlai
  • Tottenham Tana Da Damar Ɗaukar Ɗan Wasan Gefe Na Chelsea, Mykhailo Mudryk.
  • Maryam Dan’azumi Ta Koma Gida Bayan Zama Gwarzuwar Gasar Alƙur’ani
  • Goje Yace Bai Sauya Sheka Ba, Yana Shawara Kan Makomar Siyasar 2027
  • Nigeria Ta Samu Tikitin Gasar Wasan Beach Volleyball A Olympics Los Angeles 2028

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Shugaba Trump Yace Bazai Bari Iran Ta Mallaki Nukiliya Ba Amurka
  • Iran Da Amurka Zasu Kulla Yarjejeniyar Nukiliya Amurka
  • Tinubu: Mun Ware Biliyan 42 Don Inganta Lafiyar ‘Yan-Kasa Labarai
  • Ana Cigaba Da Jimamin Rasuwar Mataimakin Gwamnan Bayelsa Najeriya
  • Yanbindiga sun Kashe kimanin mutane 30 a yankin kayama ta Jihar kwaran Najeriya Najeriya
  • Shirin Safe 0500 UTC Yau Litinin 11.17.2025 Rediyo
  • Osun: Adeleke Ya Doke Oyebamiji, Ya Ci Gaba Da Rike Kujerar Gwamna Afrika
  • Jami’an Tsaro Na Amfani Da Damar Su Wajen Cin Zarafin Jama’a Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.